Muazu Hassan @ katsina times
Jaridun katsina times sun binciko don gano cikin barayin daji wa ya kai hari garin jikamshi ta karamar hukumar Musawa, jahar katsina a ranar talatar da ta gabata?
Binciken katsina Times ya gano wani barawo dake da karfi a tsakanin Musawa da Matazu mai suna Muhammadu shine wanda ya kai harin.
Binciken mu ya tabbatar Muhammadu yana cikin wadanda suka rungumi sasanci da al ummar dake yankin.
Binciken mu ya gano ,Muhammadu yana taka rawa sosai na hana wasu barayin su matsa ma yankin .ya na kuma taka rawa wajen hana bakin barayi kai hari a jahar kano.
SHANUN WAYE, SOJA SUKA KWACE?
Binciken mu ya tabbatar, Muhammadu shine ya tura da shanun da kuma yaransa, domin aje kasuwar jikamshi a sayar masa dasu.Don haka shanun sa, ne kuma yaransa suka kai shanun kasuwa
SOJAN INA NE SUKA KWACE SHANUN..?
Binciken katsina times ya tabbatar, wasu sojoji ne suka taho daga jahar kano .Ba tare da shaida ma hukumomin jahar katsina ko jami an tsaron su ba. Suka tafi da wadannan shanun suka kuma kama yaran Muhammadu da suka kawo shanun kasuwa.
ME YASA YA KAI HARI JIKAMSHI?
Muhammadu yayi zargin mutanen jikamshi sune suka gayyaci sojojin shine dalilin ya sanya ya kai masu hari.
KOMI YA LAFA ,ZAMAN SASANCI ZAI CI GABA.
Majiyoyi daban daban sun tabbatar da cewa Muhammadu ya tabbatar wa da masu shiga tsakani cewa zaman sasanci na nan daram.zai ci gaba da bayar da hadin kai
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page.katsina city news.
Katsina times @ all social media handles