An haifi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko acikin shekara ta 1865. A zamanin Sarki Muhammadu Bello ne ke Sarautar Katsina. Sunan Mahaifin shi Durbi Gidado, sunan Mahaifiyar shi Tamalamai. Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya rike mikamai da dama a lokacin mulkin Dalkazawa, kamin daga baya ya zama Sarkin Katsina acikin shekarar 1906. Daga cikin mukaman daya rike alokacin Sarkin Katsina Abubakar 1887-1905 sune Karshin Katsina Kuma Dagachin Muduru, da Danbarhim Dagacin Giremawa, sai Durbin Katsina Hakimin Mani, sannan Kuma alokacin mulkin Turawa ya zama liesin officer Tsakanin Turawan Mulkin Mallaka da Sarkin Katsina Abubakar. Yana rike da mukamin Durbi ne Turawan Mulkin Mallaka suka zo Katsina acikin shekarar 1903, a lokacin Sarki Abubakar. Turawan Mulkin Mallaka sun samu matsala da Sarki Abubakar, a inda suka tube shi daga Sarauta acikin shekarar 1905, da farko sun fara kaishi Ilorin daga baya suka dawo dashi Kano, a matsayin Dan gudun hjira. Daga nan sai suka nada kanen Mahaifin shi watau Malam Yero acikin shekarar 1905, shima Yeron cikin 1906 suka tube shi, a inda suka Tafi dashi Lokoja a matsayin Dan gudun hijira. Bayan an tube Yero sai suka ba Durbin Katsina Muhammadu Dikko Acting Emir acikin shekarar 1906, an nada shi Kuma aka bashi Sandar Girma a ranar 20 ga watan janairu, 1907.
Alhaji Muhammadu Dikko shine Sarki na 47 daga jerin Sarakinan Katsina, Kuma shine Sarki na 9 daga Sarakinan Fulani na Katsina, Kuma shine Sarki na 1, daga Sarakuna Fulani Sullubawa/Daular Dikko.
Ga kadan daga ci gaban da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya kawo a Kasar Katsina, har takai, ana Kiran Katsina da sunan Dikko, watau Katsinawan Dikko.
1. Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, shine Sarki na farko daya fara zuwa Makka a Kasar Hausa, acikin shekarar 1921. Kuma shine Sarkin daya fara Kai ziyarar aiki a Kasar Ingila, a arewacin Nigeria.
2. Shine Kuma Sarki na farko a arewacin Nigeria daya fara mallakar Mota, a lokacin mulkin Turawa.
3. A lokacin mulkin shine aka fara bude Baitul Mali na farko a arewacin Nigeria ( First Treasury) a Katsina, wanda har yanzu ginin shi na nan a Kofar soro Katsina.
4. A lokacin mulkin shine aka bude Teacher Training College ta farko a arewacin Nigeria, a shekarar 1922, wadda yawancin shuwagannin Arewa na farko suka karatu acikin ta. Daga cikin su akwai Sri, Ahmadu Bello Sardauna, da Abubakar Tafawa Balewa da sauransu.
5. Sarkin Katsina Muhammadu Dikko yayi sanadiyar kafuwar garuruwa da dama a Kasar Katsina. Daga cikin su akwai Daddara, Kurmiyar, Jibia da sauransu.
6. Ya Kuma karfafa wasan Polo a Kasar Katsina, a inda ya bude Filin wasan Polo a wajen Kofar Yandaka a shekarar 1924, wanda Katsina ta zama ja gaba ga wasan Polo a Arewacin Nigeria.
7. Bugu da Kari ya gjna babban Masallachin Juma'a a Katsina, wanda kenan Kofar soro acikin shekarar 1937. Shine ake cema Masallachin Dutsi. A halin yanzu ana Kiran shi da sunan ( Muhammadu Dikko central Mosques ).
A sabili da irin wannan ci gaban da Sarki Dikko ya kawo a Katsina, King George na Ingila ya girmama Sarki Dikko da lambar Girma ta OBE. Hakanan Kuma Kasar Katsina ta ansa sunan ta da Katsinar Dikko, mutanen Katsina Kuma ana kiransu Katsinawan Dikko.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.