Daga Katsina Times
Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa da Jaridun Katsina Times cewa Kachalla Muhammadu, shugaban wasu ’yan bindiga da ake zargin suna riƙe da Manjo Janar mai ritaya, Rabe Abubakar, ya bayyana a cikin wani saƙon murya cewa lallai Janar ɗin yana hannunsu a maboyarsu.
Majiyar ta ce a cikin saƙon muryar, Kachalla Muhammadu ya tabbatar da cewa Janar Rabe na cikin ƙoshin lafiya a inda suke tsare da shi.
A cewarsa, tun daga birnin Kaduna suke samun bayanai kan motsin Janar Rabe da lokacin da yake fita daga gida.
Kachalla Muhammadu ya bayyana cewa tun farko sun shirya kama Janar ɗin ne a kusa da mararrabar Musawa, inda hanya ke rabuwa zuwa bangarori biyu — ɗaya zuwa Musawa, ɗaya kuma zuwa Gidan Mutum Daya. Ya ce sun yi hasashen cewa Janar Rabe zai bi hanyar Gidan Mutum Daya.
Sai dai, a cewarsa, da Janar Rabe ya isa mararrabar, ya zaɓi hanyar Musawa–Matazu. Daga nan ne, Kachalla ya ce, su da wasu abokan aikinsa suka tare shi a hanya, inda suka yi nasarar kama shi.
Wannan sabon bayani da ake dangantawa da Kachalla Muhammadu ya ƙara haifar da zarge-zargen cewa akwai wata makarkashiya mai sarkakiya da ta taimaka wajen sace Janar Rabe Abubakar, musamman ganin ikirarin cewa an dade ana bibiyar motsinsa tun daga Kaduna.
A wani ƙarin bayani da Katsina Times ta samu, an ce Kachalla Muhammadu ɗan yankin Nasarawar Yamma ne, ƙarƙashin gundumar Karaduwa, da ke arewacin mararrabar Sayaya. Ana kuma kiran yankin da suna Sabon Sara.