Faruq Lawal Jobe Zai Jagoranci Tawagar Hajjin bana a Jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya nada Mataimakinsa, Faruq Lawal Jobe, a matsayin Amirul Hajjin Jihar Katsina na....

Katsina City News April 18, 2025  ·  12:00 AM
| 1,290 Views

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya nada Mataimakinsa, Faruq Lawal Jobe, a matsayin Amirul Hajjin Jihar Katsina na shekarar 2025.

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa tawagar za ta sa ido kan dukkan ayyukan aikin Hajji a gida da Saudiyya, tare da tabbatar da tsaron lafiyar maniyyata.

Mambobin tawagar sun hada da Kakakin Majalisar Jiha, Rt. Hon. Nasiru Yahaya Sai Kwamishinan Harkokin Addinai, Ishaq Shehu Dabai da wasu jami’an gwamnati da malamai.

Gwamna Radda ya yi fatan Allah ya ba tawagar nasara a aikin Hajji, inda ake sa ran za a fara nan ba da jimawa ba.

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 9 + 6?