Las Palmas, Spain – Nuwamba, 2022
Jami’an tsaron gabar tekun Spain sun ceto wasu matasa uku 'yan Najeriya da suka yi tafiyar kwana 11 a ɓoye ƙarƙashin tankin man jirgin ruwa daga Najeriya zuwa tsibirin Canary. Mutanen sun bayyana ne a lokacin da jirgin mai tutar Malta, Alithini II, ya isa tashar jiragen ruwa ta Las Palmas a tsibirin Gran Canaria.
A cikin wani hoto mai ban tsoro da hukumar kula da tsaron bakin tekun Spain ta wallafa a shafin Twitter/X, an nuna yadda mutanen uku ke zaune akan ƙaramin fili a gindin babban tankin jirgin. Rahotanni sun nuna cewa sun kwashe kwanaki kusan goma sha ɗaya ba tare da abinci mai kyau ko ruwa ba.
Bayan isar jirgin, jami'an lafiya sun karɓi masu ƙaurar domin ba su agajin gaggawa, musamman bisa la’akari da yadda jikinsu ya raunana sakamakon yunwa da ƙishirwa.
Wannan ba shi ne karon farko da aka gano irin wannan yunƙurin ɓoyewa a jiragen ruwa zuwa Turai ba. Masana harkar ƙaura sun bayyana cewa irin waɗannan hanyoyi na ɓoye kai sukan jefa mutane cikin hadari mai girma, ciki har da mutuwa kafin a kai ga isa.
Daga shafin Muhammad Cisse