Zuriyar Jarumi Kaura Amah Sun Kai Ziyara Ofishin Katsina Times Domin Godiya ga Gwamna Radda kan Daga Darajar Sarautar Dankama

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13052025_165029_FB_IMG_1747154964304.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 

A yau Talata, 13 ga watan Mayu, wasu fitattun 'yan asalin garin Dankama a ƙaramar hukumar Kaita, wadanda suka fito daga zuriyar jarumi Kaura Amah, sun kai ziyarar godiya a ofishin Katsina Times Media Group domin nuna farin ciki da godiyarsu bisa matakin da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, ya dauka na daga matsayin sarautar Dankama zuwa matsayin Hakimi.

Wannan ziyara ta gudana ne karkashin jagorancin Alhaji Musa Abdu Dankama, wanda ake yi wa laƙabi da Gwanturakin Katsina, tare da rakiyar wasu manyan ‘yan uwa da suka hada da Alhaji Isyaku Sarkin Fulani Dankama (Fasihin Kaita), Alhaji Yusuf Musa Dankama, Alhaji Aliyu Abdullahi Dankama da Injiniya Jibril I. Jibril Dankama.

A yayin ziyarar, shugabannin zuriyar sun bayyana cewa wannan mataki da Gwamna Radda ya dauka na daga matsayin sarautar Dankama ya kara wa yankin kima da daraja a idon al'umma, musamman ma a fannin al'ada da tarihi. Sun bayyana cewa tun zamanin da, Kaura Amah ya kasance jarumi mai kishin kasa da mutunci, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen zaman lafiya da ci gaban yankin.

Sun kuma yi addu’o’in fatan alheri da nasara ga Gwamna Radda, tare da neman Allah ya ci gaba da ba shi hikima da basira wajen tafiyar da jagorancin jihar Katsina cikin nasara da jin ƙai.

Bugu da ƙari, sun yaba da irin rawar da kafar yaɗa labarai ta Katsina Times ke takawa wajen watsa sahihan labarai da kuma tallata al’adun gargajiya da tarihi a jihar da ma kasa baki daya.

Ziyarar ta kasance cike da girmamawa da nishadi, inda suka sha hotuna tare da jiga-jigan ma’aikatan kafar watsa labaran, sannan suka mika gaisuwar godiya daga dukan 'yan uwa da zuriyar Kaura Amah, tare da fatan Allah ya kara zaman lafiya da ci gaba a jihar Katsina.

Follow Us