Wasu matasa da suke samun horon aikin ɗan sanda ƴan asalin jihar Katsina su kimanin Talatin da Biyar sun koka akan yadda aka sallamo su daga Police College Kaduna bisa zargin cewa tsawon su ko faɗin su bai kai abinda ake buƙata ba.
Sai dai matasan sunce anyi masu duk screening ɗin da za'a yi masu kafin su tafi su fara Karɓar horo, babu wanda yace masu suna da damuwa sai yanzu.
Matasan sunyi kira ga gwamnatin jihar Katsina da tashi cikin wannan lamarin nasu domin bin kadin abinda yake faruwa, a cewar su babu wani laifin da suka aikata in banda wannan batun da aka ambata a sama.