SANARWA TA MUSAMMAN: Muhawara Kan Karin Masarautu a Kasar Katsina
Daga: Kamfanin KATSINA TIMES Media Group
(Jaridun Katsina Times, Katsina City News, da Taskar Labarai)
Kamfanin KATSINA TIMES Media Group yana farin cikin sanar da jama’a cewa zai gudanar da muhawara ta musamman kan karin masarautu a kasar Katsina, mai taken:
"Karin Masarautu a Kasar Katsina: Tarihi, Alfanu da Illolinsa."
An shirya wannan muhawara domin bai wa kwararru da malamai daga jami’o’i da masana damar tattauna wannan muhimmin batu da ya shafi al’ummar Katsina gaba daya. Za a kuma ba kowa damar yin tsokaci da bayar da gudunmuwa ta hanyar kiran waya kai tsaye yayin da muhawarar ke gudana.
Bayanan Muhawarar:
Rana: Lahadi, 18 ga Mayu, 2025
Lokaci: Daga karfe 11:00 na safe zuwa 12:00 na rana
Lambobin Wayar Tattaunawa:
Za a watsa muhawarar kai tsaye ta kafafen:
Ana gayyatar daukacin jama’a da su shiga cikin wannan muhawara ta kafafen da aka ambata domin sauraro, tsokaci da bayar da gudunmuwa.
Bayan kammala taron, za a wallafa cikakkiyar muhawarar a shafukan yanar gizo na kamfanin domin amfanin al’umma gaba daya.
Wannan muhawara na daga cikin tsarin wayar da kan jama’a, bunkasa ilimi da karfafa ‘yancin fadin albarkacin baki – ginshikan aikin jaridun Katsina Times.