Gwamnatin jihar Zamfara ta ƙaryata wani labari da ke ikirarin cewa wata Musulma da ta zama Kirista a jihar, Zainab, za ta gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci a ranar Juma’a saboda ta sauya addini.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa rahoton tsantsagwaron ƙarya ne kuma an ɗauko shi ne daga shafukan sada zumunta da ke neman janyo cece-ku-ce.
Sanarwar ta ƙara da cewa, babu shakka an tabbatar da cewa babu irin wannan shari’a a gaban wata kotun shari’a a jihar Zamfara.
“An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran ƙarya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista.
“Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya.
“Labarin ƙaryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi ƙaurin suna wajen yaɗa labaran bogi ya yaɗa, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar ɗaukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda a ƙarshe ta gano cewa ƙarya ce kawai da Sahara Reporters ta ƙirƙira.
“Don tabbatar da gaskiya, gwamnatin jihar ta tuntubi Babban Alƙali na Kotun Shari’ar Musulunci a Zamfara dangane da irin wannan shari’a, inda ya bayyana cewa ba a taba samun irin wannan ƙara a gaban wata kotun shari’a a jihar Zamfara ba.
"Tambayar ita ce, daga ina ne wannan labari mai cike da haɗari da raba kan jama'a ya samo asali? Mene ne dalilin yaɗa shi? Mene ne masu yaɗa wannan labari suke fatan cimmawa a nan gaba?
"Muna rayuwa ne a cikin lokuta masu ban sha'awa. Kafofin watsa labarai da ya kamata su samar wa jama'a da ingantattun labarun suna zama abin kunya, sun zama masu kwafa da watsa labaran bogi don samun mabiya da 'likes'.
“Matar da aka yi amfani da hotonta wajen yaɗa labaran bogi ba ‘yar Nijeriya ba ce, sunanta Aalia, kuma ‘yar jihar Texas ce ta ƙasar Amurka.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta yi imanin cewa ya zama dole ta fayyace cewa babu wani abu makamancin haka da ke faruwa a jihar.
"Muna kira ga jami'an tsaro da abin ya shafa da su binciki tushen wannan labari na bogi, ba gaskiya ba ne, wanda ke neman haifar da tashin hankali na addini, tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a gaban kotu, dole ne mu ba da gudubmawar mu don tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan."