Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina TIMES
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruq Lawal Jobe, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da amfani da sahihan bayanai wajen tsara manufofi da aiwatar da ayyukan ci gaba a jihar.
Malam Faruq ya bayyana haka ne a daren Alhamis, 22 ga Mayu 2025, lokacin liyafar da aka shirya a fadar gwamnatin jihar domin karɓar bakuncin mahalarta Taron Kwamitin Tattaunawa na Kasa kan Kididdiga (NCCS).
A jawabin nasa, Jobe ya bayyana taron a matsayin wata dama ta musamman ga jihar, tare da yabawa mahalarta bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen bunkasa tsarin tattara bayanai da kididdiga a fadin ƙasar. “Katsina gida ce ta kowa. Mun saba da karɓar baki hannu bibbiyu,” in ji shi.
Ya jaddada cewa amfani da ingantattun bayanai shi ne jigon nasarar gwamnati, yana mai cewa gwamnatin Katsina tun bayan hawanta mulki a 2023, ta farfado da Hukumar Kididdiga ta Jiha don tabbatar da sahihancin bayanai. “Ba za mu iya tsara ci gaban tattalin arziki ba tare da sahihan bayanai ba,” in ji Jobe.
Jobe ya bayyana cewa gwamnati ta nada Farfesa Saifullah Sani a matsayin Babban Darakta na Hukumar Kididdiga ta Jiha bisa cancanta da bin doka, wanda hakan ya ba da damar gudanar da bincike a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar.
Mataimakin Gwamnan ya tabbatar wa da Shugaban Hukumar Kididdiga ta Kasa da sauran mahalarta taron cewa gwamnatin Katsina za ta duba matakan da taron ya cimma domin aiwatar da su. “Shawarwarinku za su zama tubalin gina shirye-shiryen mu,” ya bayyana.
Ya kuma tabbatar da cewa Jihar Katsina za ta ci gaba da aiki tare da Hukumar Kididdiga ta Kasa wajen ƙididdige GDP na jihar na shekarar 2024 da 2025, domin kawar da gibi a fannin tattara bayanai.
Kazalika, Jobe ya yi kira ga masu zuba jari da su mayar da hankali kan Jihar Katsina, yana mai cewa an samu ci gaba wajen tabbatar da tsaro da inganta hanyoyin rayuwa da ababen more rayuwa, wanda hakan ke ƙara jawo hankalin masu zuba jari.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Kididdiga ta Kasa, Mista Semiu Adeyemi Adeniran, ya yabawa Gwamna Dikko Umaru Radda da Mataimakinsa bisa irin goyon bayan da suke baiwa fannin amfani da sahihan bayanai wajen tafiyar da mulki. “Da dukkan jihohi suna da shugabanni kamar ku, da Najeriya ta fi gaba,” in ji shi.
Ya ƙara da yabawa jihar Katsina bisa nagarta da ta nuna wajen karɓar bakuncin wannan taro mai muhimmanci, tare da tunatar da cewa a kwanakin baya Shugaban Ƙasa ya kai ziyarar aiki a jihar domin kaddamar da manyan ayyuka. Ya kuma bukaci sauran jihohi su koyi darasi daga dabarun gwamnatin Katsina wajen amfani da bayanai da bunkasa harkokin yawon shakatawa.
A ƙarshe, Jobe ya gode wa mahalarta taron da fatan Allah Ya mayar da su gida lafiya, yana mai roƙon su da su zama jakadu wajen wanke sunan jihar daga jita-jitan rashin tsaro. “Katsina lafiya lau take, kuma kun ga hakan da idonku,” in ji shi.
Liyafar ta kasance ɓangare na kammala taron NCCS na shekarar 2025, wanda ya ƙara bayyana matsayin Katsina a matsayin jagaba a fannin tafiyar da mulki mai inganci da tsarin ci gaba na gaskiya.