Gwamnatin Katsina Ta Kara Zage Dantse Wajen Duba Cibiyoyin Koyar da Ilimin Manya a Fadin Jihar

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes03062025_182308_Screenshot_20250603-192201.jpg

Katsina TIMES 


Gwamnatin Jihar Katsina ta kara zage dantse wajen gudanar da cikakken zagayen duba cibiyoyin koyar da ilimin manya da ke cikin dukkan kananan hukumomi 34 na jihar, a wani sabon yunkuri na inganta ilimi ga kowane dan kasa ba tare da la’akari da shekaru ba.

Manufar wannan rangadi shine tantance matsalolin da ke fuskantar cibiyoyin, da tabbatar da cewa suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, musamman a yankunan karkara da ke fama da karancin kayan aiki da malamai.

Shugabar Hukumar Ilimin Manya ta Jihar Katsina, Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai, ita ce ke jagorantar wannan aiki na musamman. A wata ziyarar da ta kai daya daga cikin cibiyoyin karatu, Hajiya Bilkisu ta bayyana cewa gwamnatin Malam Dikko Umar Radda na daukar ilimi a matsayin muhimmin ginshikin ci gaban al’umma.

“Neman ilimi ba shi da iyaka ga shekaru. Burinmu shi ne kowane dan jihar Katsina ya samu ilimi mai nagarta a cikin yanayi mai inganci,” in ji ta.

A sabon zagayen da aka fi mayar da hankali a kansa, tawagar ta kai ziyara zuwa cibiyoyin da ke yankin Daura, karkashin jagorancin Malam Kabir Mamuda wanda ya wakilci shugabar hukumar, Hajiya Bilkisu. Cibiyoyin da aka ziyarta sun hada da Cibiyar Karatu ta Maibara a karamar hukumar Baure, Makarantar Malam Sani Ibrahim da Chad’i Yar Manuwa duka a karamar hukumar Sandamu.

Wasu daga cikin jami’an da suka shiga wannan duba sun hada da Kabir Mamuda, Muntari Usman, Abubakar Umar Lele, Ibrahim Abashe da Abdullahi Madugu. Suna tare da Ko’odinetan Yankin Daura, Malam Lawal Yaro Daura da jami’an kula daga yankunan Sandamu da Baure.

Ziyarar, wadda aka gudanar a ranar Asabar, 31 ga Mayu, 2025, na daga cikin tsarin da hukumar ta tsara domin duba dukkan cibiyoyin koyar da ilimin manya da ke cikin kananan hukumomi da fiye da gundumomi 60 a fadin jihar. Wannan na da nufin gano wuraren da ke bukatar gyara ko daukar matakin gaggawa.

Wannan kokari na gwamnatin jihar Katsina ya sake jaddada kudirinta na inganta fannin ilimin manya da na bai daya, wanda ke da matukar muhimmanci wajen tallafa wa ci gaban al’umma, karfafa hadin kai da kuma inganta rayuwar jama’a ta hanyar ilimi.

Follow Us