Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimes
Gwamnatin Jihar Katsina ta sake jaddada haramcin mamaye dazuka da wuraren kiwo don yin noma ba bisa ka’ida ba, tana mai bada umarnin dakatar da duk wani irin noma a irin wadannan wurare a nan take.
Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar da ya kai yankin Dawan Bai a cikin kauyen Manomawa, Unguwar Gabas Karama, da ke ƙaramar hukumar Ingawa, a matsayin wani bangare na aikin kwamitin sasantawa da Gwamna Dikko Umar Radda ya kafa domin magance sabanin da ya taso tsakanin makiyaya da wasu da ke ikirarin mallakar wani daji domin noma.
Al’ummar yankin sun kai koke kan wasu mutane da suka ce gwamnati ta mallaka musu filin dajin domin noma, duk da cewa su makiyaya ne da ke amfani da wurin wajen kiwon dabbobinsu.
A yayin tattaunawa da al’ummar, Alhaji Faskari ya bayyana cewa babu wani yanki daga cikin filayen kiwo ko dazuka da gwamnatin jihar ta bayar don noma, yana mai cewa irin wannan ikirari ba ya kan doka, kuma zai haifar da sabani tsakanin masu kiwo da manoma.
“Ina son in bayyana a fili cewa Gwamnatin Jihar Katsina ba ta ba kowa wannan fili domin noma ba. Idan ma za a raba fili, dole ne a bi doka da ƙa’idar rarraba fili na gwamnati,” in ji shi.
Ya ce daga yau, gwamnati ta soke duk wani noma da ake yi a filin da ake gardama a kai kuma ta mayar da shi hannun gwamnati domin amfanin dabbobi. “Wannan fili daga yau gwamnati ta dawo da shi, kuma an haramta ci gaba da noma a nan,” in ji shi.
Wannan mataki wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na dakile rikice-rikicen da ke afkuwa tsakanin manoma da makiyaya a karkara, musamman a wuraren da aka ware don kiwo. Gwamnatin Malam Dikko Radda ta dauki sasantawa da bin doka a matsayin hanya mafi dacewa wajen wanzar da zaman lafiya da kare hakkin kowane bangare.
Daya daga cikin wadanda suka shigar da koke, Alhaji Idi Usman, ya nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa sauraren koken su.
"Mun shigar da wannan koke ne saboda mu ne muke amfani da wannan daji wajen kiwon shanu da sauran dabbobin mu. Sai ga wasu suna cewa gwamnati ta ba su fili. Muna murna da matakin da gwamnati ta dauka domin dawo mana da hakkinmu,” in ji shi.
Sakataren gwamnati ya samu rakiyar wasu manyan jami’ai daga ofishinsa, ciki har da daraktoci daga sassan da ke da alhaki a cikin kwamitin kula da sasanci.
Gwamnati ta bukaci al’umma da su ci gaba da ba da hadin kai wajen kare muhalli da kuma hana duk wani mamaye daji ko wuraren kiwo ba bisa doka ba, tare da gaggauta kai rahoto ga hukumomi idan hakan ya faru.