KASSAROTA ta shirya taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan kiyaye hatsarurruka a hanya da inganta tsaro.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12082025_164753_FB_IMG_1755017098152.jpg

KASSAROTA Ta Gudanar da Taron Tattaunawa Kan Kiyaye Hadurran Hanya da Inganta Tsaro

Auwal Isah Musa | Katsina Times, 12 ga Agusta 2025

Hukumar Kula da Tsaro da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA) ta shirya taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar sufuri, hukumomin tsaro, da sauran cibiyoyi, domin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen rage haɗurra a hanyoyi da magance matsalolin tsaro a fadin jihar. Taron ya gudana a hedikwatar hukumar da ke kan titin Nagogo, kusa da gidan Mai na Danmarna, Katsina.

Daraktan hukumar, Manjo Garba Yahaya Rimi (mai ritaya), ya bayyana taron a matsayin wani mataki na ƙarfafa alaƙa tsakanin KASSAROTA da bangarorin da abin ya shafa a harkar sufuri, inda aka mayar da hankali kan manyan fannoni biyu, kiyaye rayuka da dukiyoyi ta hanyar bin ƙa’idojin hanya, da kuma samar da ingantaccen tsaro a fadin jihar.

“Babban burin farko shi ne tabbatar da bin ƙa’idojin hanya don rage haɗurra, asarar rayuka da dukiyoyi,” in ji shi. “Na biyu shi ne kowane bangare ya bayar da gudummawarsa wajen tabbatar da tsaro a jihar Katsina, tare da goyon bayan gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda wajen yaki da matsalar tsaro.”

Ya jaddada cewa tsaro ba aikin jami’an tsaro kaɗai ba ne, yana kira ga kowa da kowa ya bayar da tasa gudummawar duk inda yake. Haka kuma, ya bayyana wasu nasarorin da KASSAROTA ta samu, ciki har da kama motocin sata da miƙa su ga ‘yan sanda.

Mataimakin Daraktan KASSAROTA, Manjo Dahiru Mani Bagiwa (mai ritaya), ya yabawa halartar manyan bangarorin da abin ya shafa, yana mai cewa: “Idan muka haɗa hannu, muka raba bayanai, muka daidaita manufa, za mu iya samar da hanyoyi masu aminci da kuma tsare al’ummarmu daga barazanar tsaro.”

Haka kuma, Sakataren KASSAROTA, Al’amin Lawal Batsari, da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Abubakar Marwana Kofar Sauri, sun kasance a wajen taron tare da gabatar da makasudin tattaunawar tun da farko.

Taron ya samu halartar wakilai daga, Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya a jihar Katsina, Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (NSCDC), Hukumar Tsaro ta DSS, Ƙungiyar Direbobi ta NURTW, da sauran masu ruwa da tsaki da suka shafi sufuri da tsaro.

Masu ruwa da tsakin sun tattauna kan matakan hana ƙananan tashoshin mota marasa izini, tabbatar da bin dokokin jiha, da kuma gano masu amfani da harkar sufuri a matsayin ɓoye don aikata miyagun laifuka, ciki har da fataucin miyagun ƙwayoyi.

A ƙarshe, an cimma matsaya ta ƙara haɗin gwiwa da aiki tare don magance matsalolin tsaro da sufuri a fadin jihar Katsina.

Follow Us