Daga Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times
Wazirin Katsina na biyar, Farfesa Sani Abubakar Lugga, ya yi kira ga malaman addinin Musulunci da su tsare mutuncinsu a matsayin shugabanni na Addini, tare da guje wa zama cikin gwamnati ko ayyukan siyasa.
A wata tattaunawa da ya yi da Katsina Times a gidansa ranar Talata, 26 ga Agusta 2025, Farfesa Lugga ya ce yunƙurin da ake yi na haɗin kan malamai abin farin ciki ne, amma wajibi ne su kasance masu zaman kansu domin su iya kare Musulunci da Musulmai ba tare da tasirin siyasa ba.
“Mun tattauna da su sosai, na yaba da ƙudirinsu, domin a yau Musulunci na buƙatar shugabanci mai ƙarfi. Amma dole ne malamai su tsare kansu daga shiga gwamnati ko yin kwangilar gwamnati, idan ba haka ba ba za su iya yin magana kan gazawar gwamnati ba,” inji shi.
Farfesa Lugga ya yi karin haske kan tarihin shugabanci a yankin, inda ya ce kafin zuwan Turawa, sarakuna sune jagororin Musulunci, tare da malamai da limamai a matsayin abokan taya su aiki wajen tsare addini.
Ya ce abin takaici shi ne a yau, wasu shugabannin Musulmi da malaman da ke cikin ƙungiyoyin addini, musamman a Supreme Council for Islamic Affairs, dukkansu jami’an gwamnati ne. Wannan, a cewarsa, yana rage musu ikon yin magana idan gwamnati ta aikata kuskure.
“Ku duba misali, duk duniya an ƙyamaci Isra’ila, wasu ƙasashe ma sun kori jakadunsu. Amma a nan, an ga ministocinmu da jakadan Isra’ila suna taro. Abin da ya kamata ya zama nauyi ga ƙungiyoyin Musulmi su fadi albarkacin bakinsu, amma ba su yi haka ba saboda tasirin siyasa,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa yawancin manyan shugabannin Izala da Darika sun kasa yin magana akan matsalolin al’umma saboda sun tsunduma cikin kwangilar gwamnati, har ma wasu fiye da ‘yan siyasa.
“Ba wai ba mu girmama sarakuna da malamai ba ne, muna girmama su. Amma idan suka shiga aikin gwamnati, suna rasa ‘yancin yin magana a madadin al’umma. Wannan shi ne babban matsalar da ke fuskantar Musulunci a yanzu,” Farfesa Lugga ya jaddada.
A ƙarshe, ya bukaci malamai da shugabannin addini su tsaya a matsayin masu zaman kansu, masu ilimi da kishin al’umma, domin jagorantar Musulmi cikin gaskiya da adalci ba tare da rinjayar siyasa ba.