Aikin Shimfiɗa Bututun Iskar Gas na Ajaokuta--Kaduna--Kano (AKK Gas Pipeline) Yayi Nisa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02102025_094101_IMG-20230122-WA0011.jpg



Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa aikin shimfiɗa bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK Gas Pipeline) yayi nisa sosai. Wannan aiki na daga cikin manyan ayyukan raya tattalin arziƙin ƙasa da nufin kawo sauyi a fannin samar da makamashi da kuma bunkasa  masana’antu  da farfaɗo da kamfanoni  da suka daɗe da durƙushewa a Arewa.

Ministan yaɗa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai  na murnar Najeriya cika shekaru 65 da samun incin kai, wanda aka gudanar a yau Litinin, a cibiyar 'yan jarida ta ƙasa dake Abuja

Follow Us