Daga Wakilimu | KatsinaTimes
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Ahmed Muhamud Gumi, ya bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Katsina na samar da zaman lafiya, inda ya ce wannan mataki abu ne mai kyau kuma ya zo a kan lokaci, bayan fiye da shekara goma da jihar ke fama da matsalar rashin tsaro.
A wata hira ta musamman da KatsinaTimes ta yi da shi a ranar Laraba, Dr. Gumi ya ce Jihar Katsina da ma yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya sun sha wahala matuƙa sakamakon rashin tsaro, wanda ya tilasta wa dubban mutane barin gidajensu, ya kuma kawo tsaiko ga harkokin noma tare da ƙara tsananta matsin tattalin arziki.
“Fiye da shekara goma, mutane sun rasa muhallansu kuma ba su iya yin noma, musamman a wannan lokaci da tattalin arziki ke cikin mawuyacin hali,” in ji shi. “Duk wani yunƙuri na gaskiya da Gwamnatin Jihar Katsina ke yi na dawo da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba ya cancanci a yaba masa.”
Malamin ya yabawa gwamnatin jihar bisa abin da ya kira jajircewa da ƙarfin hali wajen ƙarfafa tattaunawa tsakanin ɓangarorin da ke rikici, yana mai jaddada cewa sulhu da tattaunawa su ne muhimman hanyoyi na kawo ƙarshen tashin hankali da dawo da zaman lafiya.
Sai dai Dr. Gumi ya yi gargaɗi cewa ƙoƙarin samar da zaman lafiya na fuskantar adawa daga wasu mutane da ƙungiyoyi da ke cin moriyar rashin tsaro. A cewarsa, ta’addanci da ayyukan ’yan bindiga sun rikide zuwa wata masana’anta da ake samun riba, ta hanyar safarar makamai, masu ba da bayanai da kuma amfani da kuɗaɗen gwamnati ba bisa ka’ida ba.
“Mutane da dama na cin moriyar rashin tsaro. Ya zama kamar wata masana’anta,” in ji shi. “Wasu ma na tsotsar kuɗin gwamnati da sunan tsaro. Gwamnati kanta bata san nawa take kashewa a wannan rashin tsaro ba.”
Ya kuma bayyana cewa ’yan bindiga sun shige cikin al’umma sosai, kuma suna samun makamai da harsasai daga waje, lamarin da ke ƙara rikitar da matsalar.
“Suna sayen makamai da harsasai daga ƙasashen waje. Akwai masu samarwa, masu ba da bayanai da masu taimaka musu. Wannan ne ya sa masana ke cewa rashin tsaro ya zama wata masana’anta,” in ji Dr. Gumi.
A ƙarshe, malamin ya jaddada cewa hanya mafi inganci da Gwamnatin Jihar Katsina za ta bi wajen karya wannan kasuwanci ita ce ci gaba da ƙoƙarin gina zaman lafiya ta hanyar sulhu.
“Da zarar an samu zaman lafiya, kwanciyar hankali zai dawo, sannan ci gaba zai biyo baya,” ya ƙara da cewa.
Wannan jawabi na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Jihar Katsina ke ƙara zage damtse wajen haɗa matakan tsaro da tattaunawa, domin kawo ƙarshen ’yan bindiga da dawo da rayuwa kamar yadda take a yankunan karkara.