Daga wakilanmu
Jihar Katsina ta shiga wani irin tashin hankalin siyasa da ba ta taɓa ganin irinsa ba, sakamakon ɓacin ran fitar da ’yan takarkari da jam’iyya mai mulki ta APC ta yi a makon da ya gabata.
Fushi, ɓacin rai da baƙaƙen maganganu ke fita daga bakin ’yan siyasa zuwa ƙarshen makon, abin da ya sa mutanen da suka fusata ke fita daga jam’iyyar APC zuwa wasu jam’iyyun adawa.
Jaridun KATSINA TIMES sun yi bincike mai zurfi don gano su wa suka amfana daga tikitin takarar da aka yi nasara.
A kujerun sanatoci guda uku da ake da su a jihar, ruwayoyi sun tabbatar shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ne ya nemar wa Sanata Abdu'Aziz Musa 'Yar’adua alfarmar ya koma karo na biyu.
Wasu majiyoyi sun tabbatar mana da cewa kafin wannan neman alfarmar ta fito, ana tsammanin Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bar wa Alhaji Ɗahiru Barau Mangal damar ya kawo Abbas Umar Masanawa don ya yi takarar.
Majiyoyinmu sun tabbatar mana da cewa an yi niyyar ba Mangal ne domin a ƙara jawo shi cikin tafiyar, a kuma saka masa shekaru uku ana cikin gwamnati ya zama mai biyyayya ga gwamnati da kuma jam’iyyar.
Sanatan yankin Funtua, Sanata Muntari Ɗandutse, duk da ƙorafin da ake da shi a kansa na rashin ko-in-kula da sauran ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashinsa. Misali, an ce tun da ya ci zaɓe ba a taɓa ganin shi ya kai ziyarar jaje ko ɗauki a ƙananan hukumomin Matazu, Musawa, Ƙanƙara, Faskari, Sabuwa ko Ɗandume ba.
Kamar yadda majiya mai tushe ta shaida mana, shi ma wasu dattawan yankin Funtua ne suka nemar masa alfarma.
Sanatan yankin Daura, wanda yake shi ne kakakin Majalisar Dokokin jihar Katsina, yana Majalisa tun shekarar 2015, ya zama Kakakin Majalisa a 2023. Ya kasance mai goyon bayan duk wani ƙudurin gwamnatin jiha.
Biyayya da sadaukarwar gidansu a siyasa ya sanya aka ba shi takarar.
A iya bincikenmu, duk waɗanda suka samu tikitin takarar sanatoci a APC, babu yaron gidan siyasar Dikko Raɗɗa ko ɗaya.
Tikitin ’Yan Majalisun Tarayya
Uku daga cikinsu Tinubu ya yi masu alƙawarin ba su takara ba tare da hammayya ba, bayan sun bar jam’iyyunsu na PDP suka koma APC. Su ne Mashi da Dutsi, sai Safana, Ɗan Musa da Batsari, sai kuma Bakori da Ɗanja.
Ɗaya ɗan Ɗahiru Mangal ne, wanda aka ba shi sakamakon rashin ba shi Sanata da aka yi.
Ɗaya ɗan Sarkin Daura ne. Ɗaya kuma ɗan Buhari tsohon shugaban ƙasa ne.
Wata mata da ake ta ce-ce-ku-ce a kanta, ana zargin Hadiza Bala Usman ce ta roƙar mata alfarma a wajen Gwamna.
Ɗan Arewa na Dutsinma da Kurfi, ƙarfin tasirinsa ga mutanensa ya sanya ba a cire shi ba.
Bincikenmu ya gano cikin ’yan Majalisun Tarayya 15 daga Katsina, ɗaya ne kawai ake jin yaron gidan siyasar Gwamnan Katsina ne, shi ne Aliyu Musawa, wanda ake kira da Dujiman Katsina.
Takarar ’Yan Majalisun Jiha
Bincikenmu ya gano cikin ’yan majalisun jiha 34, huɗu ne kawai ake jin yaran siyasar Gwamnan ne kai tsaye. Su ne waɗanda za su yi takara a Ɓatagarawa, Charanchi, Funtua da Bindawa. Sauran duk kamun ƙafa ne na waɗansu.
Misali, akwai ’yan majalisun da ake zargin Kakakin Majalisar Jihar Katsina ya nemar masu alfarma da tsarin cewa wai idan suna cikin majalisa za su daidaita masa ita. Daga cikinsu akwai na Safana da Mai’adua.
Akwai kuma alfarmar wasu gidajen siyasa kamar Katsina da Jibia, inda ake jin Alhaji Ɗahiru Mangal aka yi wa alfarma.
Ko An Yi Sasanci Ne Ko Zaɓe?
A iya bincikenmu, wuri ɗaya ne aka yi sasanci, ba kuma inda zaɓe ya yi aiki. Umurni ne kawai aka ba da aka sanar da wanda aka naɗa.
Misali, a zaɓen Sanata a Funtua, masu ruwa da tsaki sun yanke shawarar Hamza Sule za su zaɓa a matsayin ɗan takarar Sanata a yankin domin kamar yadda suka bayyana ya fi Ɗandutse sanin darajar mutane. Sai aka kira su a gidan gwamnati aka roƙi Hamza Sule ya janye, aka ba shi takarar ɗan Majalisar Tarayya, shi kuma Ɗandutse ya ci gaba.
A kujerar Sanatan yankin Katsina, umurni kawai aka ba da shugaban ƙasa ya roƙi a yi Abdu Soja.
A Daura kuma, har bore wasu suka fito suka yi ƙarƙashin jagorancin tsohon Kwamishinan Shari’a na Jihar Katsina, Ahmad Usman El Marzuƙ.
A Mani, an fitar da ɗan Majalisar Tarayya. Sau biyu ana zaɓe. Sau biyun duk masu ruwa da tsaki suna fitar da Ahmed Sale Jino. Daga ƙarshe aka shelanta Jamila Abdu Mani.
A Bakori, mashahuran mawaƙin nan, Dauda Kahutu Rarara har jagorantar wani ya yi ya sayo fom ɗin takara.
A ƙaramar hukumar Safana, Abdul Jalal Runka, ɗan Majalisar Jiha na Katsina, duk dattawan yankin da sarakunansu suka roƙi Gwamnan Katsina cewa ɗan Majalisar da ke kan karaga ya yi sau uku, a ba wani, amma shi aka shelanta cewa shi ne zai yi takara.
Binciken da muka gudanar mun gano cewa ban da Funtua, a duk kujerun takarar babu inda sasanci ya yi aiki, ba kuma inda zaɓe ya yi aiki.
’Yan Kwamitin Sasanci
Wasu ’yan kwamitin sasancin da muka yi magana da su bisa sharaɗin ba za mu bayyana sunansa ba, sun tabbatar mana da cewa: “An faɗa mana kai tsaye. Haƙuri za ku riƙa badawa da kuma faɗin matsayar da aka cimma, ita ce wane zai takara a yanki kaza, shi ke nan. Kuma abin da muka riƙa yi ke nan,” in ji su.
Yaran Gwamna Na Siyasa
Waɗanda suka fi fusata su ne yaran Gwamna na siyasa. Suna faɗin cewa suna bin Gwamna tsakani da Allah, sun yi tsammanin idan takara ta zo zai duba lamarinsu ya ba su su riƙe masa amana, amma ya ɗauko waɗanda kashi 90% yaƙarsa suka yi a 2023, kuma har yanzu ba su tare da shi a baɗini sai don kasuwar buƙata, su ne ya ba takara, kamar yadda suka yi zargi.
Jaridunmu sun yi magana da yawa daga cikinsu bisa amana. Ɓacin ran da ke tare da su kuwa kare ba zai ci ba.
“Mun yi nazarin duk waɗanda aka ba takara ɗaya bayan ɗaya. Mun ga dangantakarsu da Gwamna mafi yawanci dangantakar kasuwar buƙata ce, kuma wannan na nuna kamar Gwamnan na neman rushe gidansa na siyasa ne da kansa.”
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page; katsina city news
Facebook page. Jaridar Taskar labarai
Katsina times @ All social media handles.
07043777779 08057777762.