@ Katsina Times
Jaridar Daily Trust ta ranar Talata, 2 ga Yuni, 2026, ta ruwaito cewa Kachalla Muhammadu, shugaban wasu ’yan bindiga da ake zargin suna riƙe da Manjo Janar mai ritaya, Rabe Abubakar, ya bayyana cewa a shirye yake ya saki tsohon hafsan sojan idan aka saki mutanensa da ke tsare a hannun hukumomi.
A cewar rahoton, Kachalla Muhammadu ya tuntubi iyalan Janar Rabe Abubakar da ke garin Batsari, inda har ya ba su damar yin magana da shi ta waya. Rahoton ya ce Janar Rabe ya tabbatar wa iyalansa cewa yana cikin koshin lafiya kuma ana kula da shi yadda ya kamata.
An kuma ruwaito cewa Kachalla Muhammadu ya shaida wa iyalan Janar ɗin cewa idan aka saki mutanensa da ake tsare da su, shi ma zai saki Janar Rabe Abubakar ba tare da wata matsala ba.
Bugu da ƙari, ya bayyana aniyarsa ta komawa kan tafarkin zaman lafiya tare da al’ummomin yankin idan aka samu maslaha kan wannan batu.
Rahoton na Daily Trust ya ce waɗannan bayanai sun fito ne daga tattaunawar da aka yi tsakanin shugaban ’yan bindigar da iyalan Janar Rabe Abubakar.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan wannan ikirari ko yiwuwar yin musayar fursunoni ba.