An Karrama Shugaban Kamfanin Jaridun Katsina Times, Muhammad Ɗanjuma

Daga Awwal Isah da Suleiman Umar, Katsina TimesCibiyar horas da matasa sana’o’i ta gwamnatin jihar Katsina, wato Katsina Youth Craft Village, ta karrama wasu fitattun mutane biyar da suka taka…

Katsina City News October 31, 2026  ·  12:00 AM
| 66 Views
An Karrama Shugaban Kamfanin Jaridun Katsina Times, Muhammad Ɗanjuma
An Karrama Shugaban Kamfanin Jaridun Katsina Times, Muhammad Ɗanjuma

Daga Awwal Isah da Suleiman Umar, Katsina Times


Cibiyar horas da matasa sana’o’i ta gwamnatin jihar Katsina, wato Katsina Youth Craft Village, ta karrama wasu fitattun mutane biyar da suka taka muhimmiyar rawa wajen kafuwarta, ciki har da mawallafin jaridun Katsina Times, Muhammad Ɗanjuma.


An kafa cibiyar ne a shekarar 2009, kuma tun daga lokacin ta taimaka wajen horas da dubban matasa sana’o’i tare da samar musu da kayan aiki domin su dogara da kansu a faɗin jihar Katsina.


An gudanar da bikin karrama mutanen ne a wajen bikin yaye ɗalibai 1,640 da kuma raba musu kayan aikin sana’o’i na miliyoyin Naira wanda aka gudanar ranar Talata, 24 ga watan Oktoba.


Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron har da tsohon gwamnan jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, wanda aka kafa Cibiyar a lokacin mulkinsa.


Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, PhD, tare da tsohon Gwamnan, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, ne suka miƙa takardun karramawa ga Muhammad Ɗanjuma da sauran mutanen da aka karrama.


A baya, marigayi Alhaji MD Yusuf ya taɓa ɗaukar nauyin Muhammad Ɗanjuma domin gudanar da tafiya zuwa wasu ƙasashen kudancin Afirka, don nazarin matakan da suka ɗauka wajen farfaɗo da rayuwar matasansu bayan yaƙin neman ’yancin kai.


Advertisement

NRS Gateway

A yayin wannan tafiya, Ɗanjuma ya gano yadda gwamnatocin ƙasashen suka kafa cibiyoyin koyar da sana’o’i daban-daban, tare da samar da wuraren gyaran hali da sauya tunanin matasan da suka shiga harkokin shan miyagun ƙwayoyi.


Bayan dawowarsa, Ɗanjuma ya rubuta rahotannin binciken da suka bai wa gwamnatin tarayya da wasu gwamnatocin jihohi damar ɗaukar darussa daga irin waɗannan matakai.


Haka kuma, Ɗanjuma shi ne shugaban Katsina Vocational Training Centre, wata Cibiyar koyar da sana’o’i mai zaman kanta da marigayi Alhaji MD Yusuf ya kafa a shekarar 2000. 


Cibiyar ta taimaka wajen horas da dubban matasa a Katsina, tare da zama abin koyi ga sauran cibiyoyi a faɗin Najeriya.


A wajen bikin yaye ɗalibai na cibiyar a shekarar 2001, marigayi MD Yusuf ya bayyana fatansa cewa, “Fatanmu wannan Cibiyar ta zama abar kwaikwayo a duk ƙasar nan.”


Wannan buri ya samu gagarumar nasara, domin Cibiyar ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa koyon sana’o’i da dogaro da kai a tsakanin matasa.


Haka kuma, Katsina Youth Craft Village ta samu ƙarin bunƙasa a ƙarƙashin gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa, musamman ta fuskar samar da kayan aiki na zamani. 

Wannan mataki ya ƙara ƙarfafa Cibiyar wajen horas da matasa da kuma ba su damar amfani da sana’o’in da suka koya wajen inganta rayuwarsu.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 9 + 9?