Sojojin Najeriya sun ceto fasinjoji 21 da aka yi garkuwa da su a Kogi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29112025_160401_FB_IMG_1764432231232.jpg


KatsinaTimes | 29 Nov 2029

Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da ceto mutane 21 da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Obajana–Oshokoshoko da ke Karamar Hukumar Lokoja a Jihar Kogi.

Mai rikon mukamin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta Birtgade 12 da ke Lokoja, Laftanar Hassan Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Asabar yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

A baya, an rawaito cewa ’yan bindiga sun tare motoci a kan hanyar Osokoko–Obajana, inda suka yi awon gaba da fasinjoji daga motocin kasuwanci da dama, ciki har da babban motar haya mai daukar mutum 18.

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun katse hanya da misalin karfe 2:30 na rana, suka kwace motocin da suka kutsa cikin shingen da suka kafa, sannan suka yi garkuwa da fasinjojin kafin isowar jami’an tsaro.

Sai dai Laftanar Abdullahi ya ce sojoji tare da jami’an sa-kai, masu farauta da sauran hukumomin tsaro sun kutsa cikin dajin da ke yankin, inda suka yi artabu da ’yan bindigar, suka kuma ceto mutum 21.

Ya ce har yanzu ana ci gaba da aikin neman sauran mutanen da ke hannun masu garkuwa da su tare da kokarin cafke wadanda suka aikata laifin.

Wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka sace wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa dan uwansa na kan hanyarsa ta daga Owo a Jihar Ondo zuwa Abuja kafin a yi wa motar su kwanton bauna kusa da Obajana. Ya kara da cewa masu garkuwar sun tuntube shi da bukatar kudin fansa na N40 miliyan.

“Na samu kira a ranar Juma’a daga masu garkuwar da suka bukaci a biya N40 miliyan don sako dan uwana. Yana kan hanyarsa zuwa Lokoja don sanar da mahaifiyarmu game da bikin aurena na gargajiya da aka shirya yi mako mai zuwa,” in ji shi.

Shaidu sun ce motocin da lamarin ya rutsa da su sun hada da Toyota Hiace (7BGT-78LG) mai dauke da fasinjoji daga Owo zuwa Abuja; Toyota Sienna (YAB 968 AX) daga Oshogbo zuwa Kaduna; Toyota Carina (JMU 648 AA) daga Lokoja zuwa Kabba; da Toyota Hiace (GKP 178 XA) daga Abuja zuwa Ekiti, da wasu motocin ma.

Majiyar ta bayyana cewa mutum takwas daga cikin wadanda aka ceto ’yan gida biyu ne, yayin da direbobi biyu – direban motar haya da direban babban motar kaya – suma aka samu nasarar ceto su.

“Gida biyu sun rasa mutane hudu-hudu a lamarin, duk an ceto su. Haka kuma an ceto direbobi biyu da wani direban manyan motoci,” in ji majiyar.

A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ahmed Ododo, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta tsaya jiran hare-hare su faru ba kafin daukar mataki. Ya ce za a kai farmaki kai tsaye zuwa maboyar miyagun mutane.

Da yake jawabi a taron gaggawa da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya a Lokoja, gwamnan ya ce rahotannin leken asiri sun nuna cewa wasu manyan shugabannin ’yan bindiga sun shigo jihar kwanaki uku da suka gabata.

Ya ce an bibiyi muhimman kwamandojin ’yan bindigar, kuma gwamnati da hukumomin tsaro za su dauki matakin da ya dace.

“Babban kwamandan ’yan bindiga sun fara shigowa Jihar Kogi tun kwanaki uku da suka wuce. Ba za mu jira su yaƙe mu ba; mu ne za mu kai farmaki musu. Ba za mu girmama su ba, ba za mu yi sulhu da su ba, ba za mu biya kudin fansa ba. Za mu wayar da kan jama’a su kula da duk wani motsi da ba su gane ba,” in ji Gwamna Ododo.

Follow Us