Bincike Ya Nuna Cewa Ƙungiyar Da Ta Zargi Gwamna Lawal Da Yi Wa ’Yan Bindiga Afuwa Ta Bogi Ce

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes03122025_064125_FB_IMG_1764744068081.jpg



An gano cewa zargin da ake yaɗawa cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi afuwa tare da sakin 'yan bindiga da aka yanke wa hukunci ba shi da tushe kwata-kwata, bayan cikakken bincike da jaridar PremiumTimes ta gudanar kan batun da ya tayar da ƙura a kafafen yaɗa labarai.

A ranar 28 ga Nuwamban 2025, wata ƙungiya mai suna 'Human Rights Watchdog in Africa' (HRWA) ta fitar da wata sanarwa da aka ce daraktanta, Samson Adamu, ne ya sanya wa hannu, inda ta buƙaci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya ayyana dokar ta-baci a Zamfara, bisa zargin cewa Gwamna Lawal ya yi afuwa tare da sakin ’yan bindiga 69 ta sirri, ƙarƙashin wani shiri da ta kira ‘Religious Amnesty.'

Sai dai binciken da aka gudanar ya nuna cewa ba a samu asalin wannan sanarwa daga kowace sahihiyar majiya ba. Ƙokarin samun kungiyar HRWA da shugabanta Samson Adamu ya ci tura, domin babu wani ofishinta, lambar waya, shafin yanar gizo ko kuma rajistarta da aka samu a Hukumar Kula da Kamfanoni da Ƙungiyoyi ta Ƙasa. Haka nan, babu wani sahihin bayani ko sahihiyar shaidar da ke nuna wanzuwar ƙungiyar ko wannan mutum kafin ƙarshen Nuwamban 2025.

Bincike ya kuma tabbatar da cewa abin da ya faru a zahiri shi ne Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Zamfara ta taimaka wajen biyan basussukan fursunonin da aka yanke wa hukunci a shari’o’in farar hula, wanda hakan ya taimaka wajen sakin mutum 909 daga 2024 zuwa 2025. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Sakataren Zartarwa na hukumar, Habib Muhammad Balarabe, a wani taron ƙarshen shekara da aka gudanar a Gusau.

A cewarsa, a 2024 kaɗai, an biya basussukan fursunoni 473, yayin da a 2025 aka kashe Naira miliyan 67.2 domin biyan basussukan mutum 436, wanda adadin gaba ɗaya ya kai 909 cikin shekaru biyu. Hukumar ta kuma bayar da tallafin jari ga mata 200 ƙanana ‘yan kasuwa da Naira dubu 50-50, tare da bai wa wasu mata 100 kayan fara sana'a bayan kammala horarwar kiwon kaji na makonni uku.

Jami’an hukumar Zakka sun bayyana cewa ayyukansu na jinkai ba su taba shafar ‘yan bindiga da aka yanke wa hukunci kan laifukan ta’addanci ba. Wani jami’i da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, abin dariya ne ace gwamnan da ya sha bayyana a fili cewa ba ya sulhu da ‘yan bindiga shi ne zai koma ya sake su bayan an yanke musu hukunci.

Haka kuma, an tabbatar da cewa Gwamna Lawal bai taba sauya matsayarsa kan batun ‘yan bindiga ba. A ranar 29 ga Oktoban 2025, yayin da yake jawabi a gaban ɗaliban kwas ɗin tsaro a 'National Institute for Security Studies' da ke Abuja, gwamnan ya bayyana adawarsa ga yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga da ake yi a wasu jihohin Arewa maso Yamma, yana mai cewa sulhu ba tare da ƙwace makamai ba hanya ce ta jinkirta tashin hankali.

Kakakin gwamnan, Suleman Bala Idris, ya musanta zargin baki ɗaya, yana mai cewa labarin ƙirƙirarre ne da wasu ‘yan siyasa da ke cikin matsin lamba suka tsara domin bata sunan gwamnatin Zamfara.

Ya jaddada cewa babu wani lokaci da Gwamna Lawal ya yi afuwa ko ya saki kowane ɗan bindiga daga kurkuku.

Bayan kammala bincike mai zurfi, an tabbatar da cewa ƙungiyar HRWA da shugaban nata kamar fatalwa ne, kuma zargin da aka yi cewa Gwamna Lawal ya saki ‘yan bindiga ƙarya ne tsagwaron gaske.

Follow Us