Gwamnatin Tarayya Ta Ce Babu Musguna Wa ’Yan Jarida a Mulkin Tinubu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes03122025_064917_FB_IMG_1764744542545.jpg



Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida, kare dimokiraɗiyya, da tabbatar da tsaro a fagen yaɗa labarai a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a Taron Shekara-shekara na Cibiyar 'Yan Jarida ta Duniya (IPI) da aka gudanar a ranar Talata a otal ɗin NICON Luxury da ke Abuja.

Idris ya bayyana kafofin watsa labarai a matsayin “hanyar sadarwa mafi muhimmanci ta kowace dimokiraɗiyya, kuma mai ƙara ƙarfafa muryar ’yan ƙasa.”

Ya ce halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wajen buɗe taron ya nuna yadda gwamnati take buɗe ƙofa ga tattaunawa da manema labarai.

Da yake magana kan taken taron, wato “Magance Musguna Wa Kafofin Watsa Labarai a Nijeriya,” Ministan ya ce dole ne a bambanta abubuwan da suka faru a baya da kuma yanayin da ake ciki a yau.

Ya bayyana cewa, “Babu wata manufa ta gwamnati da ke neman takura kafofin watsa labarai a yau,” yana mai cewa hujjoji suna nuna kamewa da haɗin kai, ba ƙiyayya ba.

Ya ce: “Tattaunawa kan ’yanci dole ta ta’allaƙa ne a kan gaskiya. Idan wani ya yi iƙirarin cewa akwai wata manufa ta musgunawa a yau, ya kamata mu auna wannan iƙirari da hujjoji.” 

Idris ya ce hukumomin tsaro yanzu suna aiki ne ƙarƙashin ƙa’idoji masu tsauri domin tabbatar da amincin ’yan jarida, musamman a lokutan zanga-zanga ko wuraren da ake ganin rikice-rikice.

Ya kuma bayyana cewa hukumomin da ke kula da yadda kafafen yaɗa labarai ke aiki suna ci gaba da samar da muhallin da ya dace, mai tsari da gaskiya.

Ya ce: “’Yantar da kafofin watsa labarai abu ne da ba za a iya watsar da shi ba. Dole ne ’yan jarida su iya yin aikin su ba tare da tsoratarwa ko tsoma baki ba, kuma wannan gwamnati ta kasance a ko da yaushe a kan wannan matsayi.” 

Ya kuma ambaci wani rahoto da wata jarida ta wallafa rahoto mara kyau da ya yi iƙirarin cewa wai Nijeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ke tilasta karɓar haƙƙin 'yan luwaɗi da maɗigo.

Ya ce duk da cewa rahoton na iya tayar da rikicin addini da al’ada, gwamnati ta zaɓi gaskiya maimakon husuma.

Idris ya ce: “Gwamnatin Tarayya ta buga cikakken rubutun yarjejeniyar, ta fitar da bayanai na gaskiya, ta tattauna da jama’a a fili, sannan ta kai ƙorafi ta hanyar mai duba aikin jaridu mai zaman kan sa. Ba mu yi amfani da matsin lamba ko tilastawa ba. Mun zaɓi gaskiya.” 

Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya za ta karɓi baƙuncin Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai (IMIL) na Afrika, wadda za ta riƙa horar da ’yan jarida, malamai, da al’umma kan yadda ake yin aikin jarida cikin gaskiya, tantance bayanai, da yaƙi da yaɗa ƙarya bisa tsarin al’adu na Afrika.

Ya ce cibiyar za ta kasance mai zaman kan ta, wadda ke dogaro da ilimi ba tare da zama mai magana da yawun gwamnati ba. 

Ya ce za a ƙaddamar da ita a farkon watannin 2026.

Haka kuma, Idris ya tabbatar da shirye-shiryen gwamnati na yin aiki tare da IPI reshen Nijeriya, Ƙungiyar Editocin Nijeriya, da Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya domin sabunta tsarin dokokin kafafen yaɗa labarai bisa ƙa’idojin duniya, tare da kiyaye ’yancin magana da muradun jama’a.

Ya ce: "Haƙƙin mu mu duka ba wai kawai ƙalubalantar musgunawa ba ne, har ma da faɗaɗa 'yanci. Mu ƙarfafa ginshiƙan dimokiraɗiyyar mu ta hanyar kare 'yancin da ke tabbatar da dorewar ta.” 

Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda shi ne ya jagoranci buɗe taron.

Follow Us