Rundunar ‘Yan Sanda ta Borno Ta Gano Zinari da Aka Boye Shekaru 15 da Suka Gabata

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02122025_104207_FB_IMG_1764671821242.jpg

Katsina Times 

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Borno ta bayyana cewa ta gano kayayyakin zinariya da suka kai kimanin naira miliyan 23.6, da wata mata ta boye shekaru 15 da suka gabata a lokacin da ta gudu sakamakon harin Boko Haram a garin Mallamfatori.

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a ranar 1 ga Disamba 2025, rundunar ta ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya jinjinawa DPO na Mallamfatori da tawagarsa bisa kwarewa da gaskiya wajen gano kayan.

Sanarwar ta bayyana cewa matar da ta tsere daga garin lokacin harin Boko Haram, ta dawo kwanan nan domin neman taimakon rundunar wajen gano wasu kayayyaki da ta binne a cikin kasa lokacin arangamar.

Bayan bincike da kokarin hadin gwiwa, jami’an ‘yan sandan suka gano zinari mai nauyin 22cc da kimar naira miliyan 20, da kuma dandantsen zinare tare da sarka da kimarta ta kai naira miliyan 3.6.

Kwamishinan ya yaba da gaskiya da sadaukarwar jami’an, yana mai cewa wannan aiki ya kara tabbatar da dabi’un da rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ke alfahari da su, tare da karfafa amincewar jama’a ga jami’an tsaro.

CP Abdulmajid ya sake jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai domin inganta tsaro a jihar.

Follow Us