Tarihin Rayuwar Ganar Christopher Musa: Sabon Ministan Tsaro na Najeriya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02122025_161551_FB_IMG_1764692058373.jpg


An haifi Janar Musa a ranar 25 ga Disamba, 1967, kuma a yau yana da shekaru 58. Ya yi digirinsa na farko a Nigerian Defence Academy (NDA), Kaduna, inda ya kammala a 1991. Kafin shiga NDA, ya yi karatun gaba da sakandare a College of Advanced Studies, Zaria a 1986, bayan kammala karatunsa na firamare da sakandare a Sokoto.

Janar Musa ya yi fice a manyan mukamai da dama a rundunar sojan Najeriya, inda ya taka rawa a yaki da ta’addanci da kuma gina karfin sojoji:

Babban Hafsan Tsaro — 2023 zuwa 2025

Ya jagoranci rundunonin sojin ƙasa, ruwa da sama, tare da mayar da hankali kan tsare-tsaren tabbatar da tsaron kasa da inganta hadin kai tsakanin bangarorin tsaro.

Kwamandan Infantry Corps — 2022 zuwa 2023

Ya jagoranci cibiyoyin horaswa da bunkasa dabarun sojin kasa.

Theatre Commander, Operation Hadin Kai — 2021 zuwa 2022

Ya jagoranci yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas, musamman yankin Tafkin Chadi.

Kwamandan Sector 3, Multinational Joint Task Force — 2019 zuwa 2021

Ya hada kai da kasashe makwabta wajen kawar da barazanar ta’addanci a yankin.

Sauran Manyan Mukamai

Ya rike mukamai irinsu:
 • Kwamandan 73 Battalion
 • Deputy Chief of Staff, Training and Operations

Assistant Director, Army Policy and Plans
Member, Training Team of the Armour Corps

Tun daga lokacin da aka yi masa bada umarnin soja a 1991, ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka gina masa gogewa ta musamman wajen yaki, tsare-tsare, da horaswa.

Lambobin Yabo da Karramawa

A 2012, Janar Musa ya samu Colin Powell Award for Soldiering, lambar yabo da ke girmama jaruntaka da jajircewa wajen murkushe ayyukan ta’addanci.

Muhimman Nasarori

Ɗaya daga cikin manyan jagororin da suka yi tasiri a yaƙin ta’addanci a Arewa maso Gabas. Ya bunkasa sabbin tsare-tsaren horaswa da dabarun yaki masu inganta tsaron kasa.

Nadinsa a matsayin Babban Hafsan Tsaro a 2023 ya nuna cikakken amincewar Shugaba Tinubu ga kwarewarsa da hangen nesa.

Follow Us