Ministan Sadarwa, Kirkire-Kirkire da Tattalin Arzikin Dijital na Najeriya, Dr. Bosun Tijani, ya kai ziyara ta musamman a cibiyar KATDICT da ke birnin Katsina, inda ya yaba da ayyukan cigaban fasaha da cibiyar ke gudanarwa, tare da yin alkawarin kafa Dakin Kirkira (Maker Lab) na zamani a jihar Katsina.
Ziyarar ta gudana ne a ranar Asabar ," kamar yadda Babban Daraktan KATDICT, Naufal Ahamed, ya bayyana a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook, inda ya bayyana wannan rana a matsayin mai tarihi da cike da alƙawurra ga matasa da al'ummar jihar.
“A yau mun samu babban ɗaukaka na karɓar bakuncin Mai Girma Ministan Sadarwa a hedikwatar mu ta KATDICT da ke Katsina,” in ji Naufal.
A yayin ziyarar, Ministan ya gana da matasan shirin 3MTT (Three Million Technical Talent), shirin gwamnatin tarayya da ke horar da matasa a fannoni daban-daban na fasaha da dijital. Haka kuma, ya zagaya sassa daban-daban na cibiyar, ciki har da ɗakunan kirkire-kirkire da horarwa, inda ya ji ta bakin masu gudanar da ayyuka kan burin KATDICT na gina Katsina mai dogaro da ilimi da fasahar zamani.
A jawabinsa na musamman, Naufal Ahamed ya bayyana irin rawar da cibiyar ke takawa wajen mayar da jihar Katsina cibiyar kirkira da dijital, wacce ke amfani da basira da kwazon matasa wajen inganta tattalin arziki da rayuwa.
Minista Tijani, cikin jawabin martani, ya bayyana gamsuwarsa da abin da ya gani, inda ya ce:
“Wannan ita ce Katsina mai cike da dama marasa iyaka, wadda fasaha da shugabanci mai hangen nesa ke motsawa.”
Baya ga yaba wa aiki, Ministan ya bayyana shirinsa na haɗa gwiwa da KATDICT wajen gina babban Maker Lab na zamani – wani wuri da zai bai wa matasa damar koyon fasaha, kirkira, da gina sabbin hanyoyin zamanance.
Shirin 3MTT (Three Million Technical Talent), wani muhimmin shiri ne na gwamnatin tarayya da ke da nufin horar da matasa miliyan uku a fannonin fasaha kamar: shirye-shiryen kwamfuta, bayanai (data), kirkira, da sauran fasahohin zamani. Wannan zai basu damar shiga kasuwar aiki ta zamani da kuma ƙirƙiro ayyukan yi.
Maker Lab kuwa, dakin kirkira ne da ke cike da kayan zamani kamar na'urar buga 3D, na’urorin lantarki, da sauran kayan fasaha, wanda ke bai wa matasa da ƙwararru damar koyon sabbin dabaru, ƙirƙira sabbin abubuwa, da gina ayyuka na kirkire-kirkire.
A cewar Naufal Ahamed, wannan ziyara da alƙawarin Ministan ya zama jigon sauyi, ba wai kawai ga KATDICT ba, har ma da matasan da ke da mafarkin samun makoma a duniyar dijital daga cikin jihar Katsina.
“Wannan wata mahimmiyar dama ce ta gina makoma tare, mu gina Katsina da ke cike da dama ga kowane matashi,” in ji shi.
Ziyarar da Ministan ya kai tana ƙara karfafa gwiwar KATDICT wajen cika burin ta na kawo sauyi ta hanyar ilimi, fasaha, da haɗin gwiwa, da kuma tabbatar da cewa matasan Katsina sun samu gagarumar dama a duniyar kirkira da dijital.