Zargin Garkuwa da Fyade: Sarkin Daura Ya Tube Dagacin Mantau Daga Sarauta

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes19052025_194803_FB_IMG_1747683422315.jpg


Auwal Isah | Katsina Times. 

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji (Dr) Faruq Umar Faruq CON, ya tube Iliya Mantau daga sarautar Dagacin Mantau garin ‘Yarmaulu, dake karamar hukumar Baure a jihar Katsina, sakamakon zarge-zargen hannu da ake masa a cikin garkuwa da wata mata da kuma yi mata fyade.

An sanar da dakatarwar a ranar Litinin, bayan samun koke-koke daga al’ummar garin wanda ya kai ga zanga-zangar matasa a makon da ya gabata. Matasan sun bayyana damuwarsu kan yadda ake zargin dagacin da hannu kai tsaye cikin lamarin da ya hada da sace matar aure mai suna Zulaihatu tare da dan jaririnta, da kuma yi mata fyade bayan karbar kudin fansa.

Sarkin Daura, a lokacin da yake sanar da tsige Dagacin, ya jaddada cewa masarautar Daura ba ta lamunci duk wani abu da zai tauye rayuwar talaka, yana mai cewa kofar masarautar a bude take ga kowane dan kasa da ke da korafi ko koken zalunci.

“Idan wani ya ji an cuce shi, ko da dan da na haifa ne, ya zo ya gabatar da korafinsa a masarauta. Wannan masarauta ce ta talakawa,” in ji mai martaba Sarkin.

Ya kara da bayyana cewa: “Wannan masarauta ta taba tube wanda ta nada, kuma Sarki Abdurrahman ya taba daure dansa a bisa laifi. Shi ya sa ba za mu lamunci cin zarafin kowa ba.”

Sarkin ya bayyana cewa, daga ranar Litinin, Iliya Mantau ya daina zama Dagaci a masarautar Daura, yana mai cewa za a nada sabon wakili a garin domin ci gaba da gudanar da harkokin sarauta bisa gaskiya da adalci.

A karshe, Sarkin ya ja hankalin jama’a da su guji yada jita-jita da ba ta da tushe, ya kuma bukaci su ci gaba da nuna biyayya ga doka da oda, tare da kai koke-kokensu ta hanyoyin da suka dace domin a bi masu hakkinsu.

A baya-bayan nan, jaridar Katsina Times ta rawaito yadda wasu matasa suka gudanar da zanga-zanga a garin ‘Yarmaulu, inda suka zargi Iliya Mantau da wasu mutane da hannu cikin garkuwa da wata mata da danta, tare da fyade bayan karbar kudin fansa Naira miliyan 20, Zargin ya janyo cece-kuce, kasancewar masarautar ta gaza daukar mataki na tsige dagacin cikin shekara guda da faruwar lamarin, duk da cewa batun na kotu.

Follow Us