Auwal Isah Musa | Katsina Times
An kaddamar da Kamfanin samar da Garin Filawa, Masara da sauran na'ukan abincin dabbobi a jihar Katsina.
Kamfanin mai suna 'TFK Maize Flour Mills', an kaddamar da shi a ranar Litinin din nan a harabarsa da ke garin shinkafi, kan hanayar zuwa karamar hukumar Kaita.
Da yake jawabi game da yadda ya samar da Kamfanin, Ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar, ya bayyana cewar wannan shiri na kafa Kamfanin ya samo asali ne tun sama da shekaru 30 da suka gabata, yana mai bayyana cewar sai yanzu ne Allah ya sa a cimma nasarar aiwatar da shi.
Ambasa Ahmad Rufa'i, ya bayyana Kamfanin a matsayin wata alama ta habaka samar da ingantaccen abinci ga 'yan jiha da kasa baki daya, da raya tattalin arzikin al'ummar da kuma samar da aikin yi ga matasa.
Ya kuma gode wa gwamnan jihar, Masarautar Katsina, da kuma Attajiri Alhaji Dahiru Mangal bisa ga goyon baya da suka ba shi har Kamfanin ya kammalu tade da cika dukkan abubuwan da ake bukata.
Gwamna Radda a yayin jawabinsa a wajen, ya yaba wa shugaban Kamfanin Ambasada Ahmed Rufa'i bisa ga samar da wannan Kamfani a jihar, inda ya bayyana shi a matsayin mai kishin jihar.
Ya ce, duk da mai kamfanin yana da damar da zai iya zuwa wani waje ya gina abinsa, amma ya zabi ya yi shi a cikin jiharsa don al'ummar jihar su ci moriyarsa. Gwamnan Radda ya bayyana Kamfanin a matsayin wanda zai kawo ci gaban tattalin arziki ga jihar, wanda da ma ana da kishirwar ire-irensa.
"A yau, muna bukatar ire-iren wadannan Kamfani wanda zai kawo ci gaba da raya tattalin arziki a jiharmu.
"A mamadina da gwamnatin jihar Katsina, muna jinjina maka bisa ga wannan babban ci gaba da ka samar mana." Ya gode masa.
Bikin kaddamar da Kamfanin ya samu halartar Jami'an gwamnatin jihar da na makwabtan jihohi, shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya, 'yankasuwa, shugabannin al'umma, masu zuba hannun jari, da sauransu.