Daga Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times
Mai ba Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda shawara kan harkokin jam’iyya, Hon. Shafi’u Duwan, ya bayyana gwamnatin Radda a matsayin sabuwar gwamnati da ta sha banban da gwamnatocin da suka gabata a jihar Katsina.
A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Katsina Times, Hon. Shafi’u ya ce gwamnatin Radda ta kawo sauye-sauye da dama, musamman wajen tallafa wa matasa ta hanyar samar da ayyukan dogaro da kai da kuma inganta hanyoyin rayuwa a jihar. Ya ce kusan kowane fanni na gwamnatin yanzu akwai gagarumar ci gaba da za a iya tattaunawa akai tsawon lokaci ba tare da an kammala ba.
A cewarsa: “Idan muka duba fannin gyara da cigaban da Gwamna Radda ya kawo a harkokin gudanar da gwamnati, to abin a yaba ne. A baya, idan kana da kusanci da wani babban ɗan siyasa, cikin kankanin lokaci za ka iya zama Permanent Secretary ko Director. Amma yanzu sai wanda ya cancanta, sai ka rubuta jarabawa sannan za ka samu mukami.”
Ya ci gaba da bayyana cewa: “Tun daga shekarar 1999, ba a taɓa samun wani gwamna da ya ɗauki malaman makaranta har mutum dubu bakwai a lokaci guda ba, sai wannan gwamnatin Radda. Kuma wannan babbar nasara ce da aka cimma a cikin shekaru biyu kacal da ya hau mulki.”
Kan sha’anin tsaro kuwa, Hon. Shafi’u ya bayyana cewa Gwamna Radda ya taka rawar gani: “Kowa ya san halin da ake ciki lokacin da ya karɓi mulki, amma cikin ɗan kankanin lokaci ya shawo kan matsalolin tsaro da kaso mai yawa. Daukar matasa dubban a matsayin ma’aikatan Community Watch Corps nasara ce babba. Gwamna ya ba su horo, ya kuma samar musu da kayan aiki. Mutanen da aka ɗauka daga yankunan da ke fama da matsalolin tsaro ne, don haka suna da kwarin gwiwar kare yankunansu.”
A fannin lafiya kuwa, ya ce Gwamna Radda ya bada gagarumar gudummawa: “Ya gyara asibitoci, ya samar da magunguna da kayayyakin aiki na zamani. A kusan kowace karamar hukuma, akwai asibitoci guda biyu zuwa uku da aka daga matsayin su zuwa manyan cibiyoyin lafiya.”
Hon. Shafi’u ya ƙare da cewa gwamnatin Radda na tafiya bisa tubalin gaskiya da cancanta, kuma tana da burin inganta rayuwar al’ummar jihar Katsina ta fannoni daban-daban.