Hukumar Kula da Tsaro da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA) ta sake jaddada kudirinta na rage haɗurra a kan hanya da tabbatar da bin ƙa’idar zirga-zirga a faɗin jihar, yayin da ta karɓi baƙuncin tawagar Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Ƙasa (PCC) a wata ziyarar girmamawa.
Daraktan Hukumar KASSAROTA, Manjo Garba Yahaya Rimi (Mai Ritaya), ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karɓar tawagar PCC a hedikwatar hukumar da ke Katsina. Ziyarar na da nufin ƙarfafa fahimtar juna da kuma duba hanyoyin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin biyu.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na KASSAROTA, Abubakar Marwana Kofar Sauri ya fitar, Manjo Rimi ya bayyana cewa KASSAROTA tana aiki ne da cikakkiyar doka da tsarin da gwamnatin jihar ta gindaya mata. Ya ce aikinta ya ta’allaka ne kan kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da ilmantar da su kan mahimmancin kiyaye doka a hanya.
“Ayyukan KASSAROTA sun shafi duk wani nau’in sufuri a cikin jihar. Duk wanda ya hana jami’an KASSAROTA aiwatar da aikinsu, to yana karya doka ne kai tsaye,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, manufar hukumar ba ta tsaya ga tilastawa kawai ba, har ma tana mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a da tabbatar da tsari da zaman lafiya a hanyoyi.
Da yake magana a madadin tawagar PCC, shugabannin tawagar sun yabawa yadda KASSAROTA ke gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da nagarta, tare da nuna jin daɗi kan tsarin da hukumar ke amfani da shi wajen gudanar da aiki.
Hukumomin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi haɗin gwiwa, musamman yadda za a ƙarfafa bin doka da ƙarfafa amana a cikin hukumomi domin inganta ayyukan jin ƙai ga al’umma.
Ziyarar na daga cikin matakan da ke nuni da ƙoƙarin hukumomin wajen ƙarfafa aiki tare domin inganta tsaron hanyoyi da kyautata hidimar gwamnati ga jama’a a Jihar Katsina.
Hoto: KASSAROTA