An Yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Kurfi Kan Sulhu da Ayyukan Ci gaba

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29082025_104003_Screenshot_20250829-113822.jpg


Daga Katsina Times

Ɗan siyasar Kurfi kuma jigo a siyasar jihar Katsina, Alhaji Shuaibu Iliya da aka fi sani da Shagali, ya jinjinawa shugaban karamar hukumar Kurfi, Hon. Babangida Abdullahi Kurfi, bisa nasarar da ya samu wajen gudanar da sulhu da Fulani makiyaya masu ɗauke da makamai.

Da yake magana da jaridar Katsina Times, Shagali ya ce wannan sasanci zai taimaka wajen bunƙasa harkokin noma, kasuwanci da zirga-zirga a cikin karamar hukumar, tare da samar da kwanciyar hankali.

Ya ƙara da cewa zaman lafiya da wannan sulhu ya haifar zai dawo da zumunci tsakanin al’ummar Kurfi, wanda matsalar tsaro ta kawo tsaiko a kansa a baya.

A cewarsa, tun bayan darewar Babangida Kurfi kan mulki, ya rika aiwatar da tsare-tsaren ci gaba da suka inganta darajar karamar hukumar da kuma rayuwar jama’arta.

Shagali ya yi kira ga mazauna Kurfi da su ci gaba da mara wa shugaban baya, domin ganin an dore da cigaba da jin daɗin da al’umma ke amfana da shi.

Follow Us