@ www.katsinatimes.com
Facebook page: katsina city news
Wani bincike da jaridar Katsina Times ta yi, ya gano akwai yiyuwar jam’iyyar adawa su ƙwace ƙaramar hukumar Jibia ta Jihar Katsina, in har aka ci gaba da tafiya yadda ake a siyasance da kuma mulki.
Bincikenmu ya gano akwai bambanci mai faɗi da kuma nuna wariya a tsakanin al’ummar Jibia cikin gari da kuma karkara.
Al’ummar karkara na ƙaramar hukumar Jibia na ƙorafin cewa duk wani muƙami da ci gaban ƙasa ana tattara shi ne a Jibia “Ward A and B”, wadda ita ce ƙwaryar birnin Jibia.
Bincikenmu ya tabbatar da cewa ɗan Majalisar Tarayya, da ɗan Majalisar Jiha mai wakiltar Jibia, da shugaban ƙaramar hukumar Jibia, da Kwamishina, da mai ba Gwamnan Katsina shawara, da shugabannin jam’iyya duk daga Jibia “Ward A and B” suke.
A iya bincikenmu, mun gano ɓacin rai da fusata a fuskokin al’ummar sauran yankunan sakamakon wannan wariya da suke zargin ana nuna masu.
Hatta ayyukan ci gaba da raya ƙasa, al’ummar sauran yankin suna nuna ba su san wani romon dimokuraɗiyya ba.
Bincikenmu ya tabbatar har ma da ’yan bokonsu da attajiransu suna wannan ƙorafi, inda a bayyane suke magana da jaridar Katsina Times cewa, “A gyara ko mu nemar wa kanmu mafita.”
’Yan Jibia “Ward A & B” suna iƙirarin su ne suka fi yawan ƙuri’u, shi ya sa suke da ɗabi’ar mai rinjaye shi ne ke da ƙarfi.
Iƙirarin da sauran al’umma suka ƙaryata, inda suka ce ai mutanen karkara su ne ke fitowa su jefa ƙuri’u. Na cikin gari ba su taɓa goyon bayan jam’iyya mai mulki ba, kuma a je a duba tarihin zaɓukan baya.
Bincikenmu ya gano jam’iyyun adawa na farautar waɗannan al’umma sosai, suna neman tsayar musu da ’yan takara ’yan son al’umma don ba su cikakkiyar dama.
Mun yi ƙoƙarin magana da shugaban ƙaramar hukuma ko shugaban jam’iyyar APC mai mulki, amma haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.
Ko Jibia na cikin inda jam’iyyar adawa za ta ƙwace a zaɓen 2027? Lokaci ne zai tabbatar da hakan.