An Fitar da Sunayen Wadanda Suka Tsallake Jarabawar CBT a Daukar Malaman Makaranta A Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11052026_215223_IMG-20260503-WA0299.jpg



Katsinatimes 

Kwamitin da gwamnatin Jihar Katsina ta kafa domin gudanar da aikin daukar malaman makarantu ya sanar da fitar da sunayen wadanda suka tsallake jarabawar Computer-Based Test (CBT) a aikin daukar malaman firamare da sakandare a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da sakataren kwamitin, Dakta Isah Idris Zakari, ya sanya wa hannu, an bukaci dukkan masu neman aikin da su shiga shafin daukar aikin domin duba matsayinsu tare da sauke takardar gayyata (interview slip).

Sanarwar ta ce ana iya shiga shafin ta wannan hanya: katsinasemis.com/nterview

Kwamitin ya bayyana cewa takardar (Interview) na dauke da bayanan ranar, wurin gudanarwa da kuma lokacin da aka ware wa kowanne Mai sha'awar.

Haka kuma, an umarci wadanda aka gayyata da su je wajen tantancewa tare da asalin takardun karatunsu da na kwarewa, tare da ingantacciyar shaidar tantancewa.

Sanarwar ta kara da cewa daukar malaman na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na inganta bangaren ilimi ta hanyar samar da kwararrun malamai a makarantun jihar.


Follow Us