A wani mataki na tallafa wa addinin Musulunci, Alhaji Abdul Aziz Mai Turaka ya kammala aikin samar da rijiyar burtsatse da kuma wutar lantarki ta hasken rana (solar) ga wani masallaci da ke unguwar Daki Tara, Kofar Kaura a cikin karamar hukumar Katsina.
An mika aikin ne a safiyar Lahadi, 6 ga Yuli, 2025 ga kwamitin gudanarwar masallacin, inda aka bayyana cewar kudaden aikin sun fito ne daga aljihun Alhaji Abdul Aziz Mai Turaka kai tsaye.
A cikin aikin, an gina rijiyar burtsatse, an girka tanki, famfuna, da kuma tsarin wutar lantarki ta solar domin samar da ingantaccen ruwa da hasken lantarki ga masallacin da ma al’ummar yankin gaba ɗaya.
Da yake jawabi yayin karɓar aikin a madadin kwamitin masallacin, shugaban gudanarwar masallacin, Malam Hadi Balarabe, ya nuna godiya tare da yi wa Alhaji Mai Turaka addu’ar samun lada mai yawa bisa wannan hidimar alheri da ya yi wa al’umma.
Haka zalika, Malam Hadi ya yaba da gudummawar wadanda suka assasa masallacin da kuma masu ci gaba da tallafa wa harkokinsa, yana mai fatan Allah ya saka musu da alheri.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Katsina, Hon. Isa Miqdad AD. Saude, ya mika aikin a madadin Alhaji Abdul Aziz Mai Turaka, inda ya jinjina masa bisa wannan aiki na alheri da ya saba gudanarwa a cikin al’umma.
A nasa bangaren, Alhaji Abdul Aziz Mai Turaka ya bayyana farin cikinsa kan yadda kwamitin masallacin ya zabe shi domin gudanar da aikin. Ya ce irin wannan aikin na alheri ba kowa Allah ke nufar ya yi ba, sai wanda Allah ya zabo.
Ya kuma bada tabbacin cewa kofarsa a bude take a kowane lokaci idan aka bukaci taimako wajen gudanar da ayyukan alheri, musamman domin ci gaban addinin Musulunci.
Daga ƙarshe, Alhaji Mai Turaka ya roƙi kwamitin masallacin da su bude rijiyar domin amfanin al’ummar yankin ta yadda za su rika samun ruwa cikin sauki a kullum.