ANAN Ta Kammala Taron Horo Na MCPD a Katsina Da Kiran Tabbatar Da Harsashin Gaskiya, Kwarewa Da Cigaban Kasa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09072025_204740_FB_IMG_1752093961288.jpg



Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina TIMES – 9 ga Yuli, 2025

Kungiyar Akantoci ta Kasa (ANAN) ta kammala zaman taron horo na shekarar 2025 a ƙarƙashin shirin "Mandatory Continuing Professional Development" (MCPD) a garin Katsina, inda aka sake jaddada muhimmancin kwarewa, tsayawa kan gaskiya da kuma bayar da gudunmuwa wajen ci gaban ƙasa.

Taron wanda ya gudana na tsawon kwana huɗu daga ranar Lahadi 6 zuwa Laraba 9 ga Yuli, ya samu halartar manyan akantoci daga sassa daban-daban na Najeriya, shugabanni na gwamnati, dalibai da kuma sarakunan gargajiya, a dandalin tarurruka na (Continental Events and Sports Centre) da ke Katsina.

Taken taron shine: “Haraji da Bin Doka: Dabarun Girmama Harsashin Sana’ar Akantanci a Zamanin Sauyin Fasaha”, inda aka mayar da hankali kan rawar da akantoci za su taka wajen tabbatar da gaskiya da bin ka’ida a harkokin mulki.

A jawabinta na rufe taron, Shugabar kungiyar ta ANAN, Hajiya Rakiyat Talatu Kishimi, FCNA, ta jinjina wa sabbin mambobi da suka samu shaidar zama cikakkun 'yan ANAN, tare da bukatar su cigaba da dagewa a kan bin doka da tsare-tsaren ƙungiyar.

“Taron MCPD ba al’ada ce kawai ba. Wata hanya ce ta ƙara haɗa zumunci da kuma gina sabbin hazikai da za su tsare amanar kasarmu ta hanyar gaskiya da amana,” in ji ta.

Shugabar ta bukaci dukkan mambobin ANAN da su rika halartar ayyukan rassan kungiyar, tana mai cewa zama cikin sahihin reshi da biyan kuɗin membobinsu wajibi ne.

“Hukumar ku a matakin reshi ce za ta ba da shaida idan wata hukuma ta bukaci bayani a kanku. Don haka, ku zama masu hulɗa da rassan ku, ku san lambarku na memba, domin shi ne sabon sunanku,” ta jaddada.

A ranar Talata 8 ga Yuli, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya buƙaci akantoci su rika taka rawa wajen inganta gaskiya da ingantaccen shugabanci a matakin gwamnati.

“Ku ne tubalin gaskiya a cikin tsarin gwamnati. Ba kawai sana’a kuke yi ba ku ne masu kare dukiyar jama'a,” in ji Gwamnan.

Ya bayyana wasu daga cikin muhimman matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wajen yaki da cin hanci da rashawa, ciki har da kafa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci ta Jiha, aiwatar da "Treasury Single Account" (TSA) da kuma shiga tsarin Open Government Partnership (OGP).

Shugabar ANAN ta yabawa gwamnatin jihar bisa goyon bayan da take bai wa ƙungiyar, tana mai cewa “Gwamnatin Radda na bayar da misali wajen aiwatar da sauye-sauyen ci gaba.”

Shugaban kwamitin shirya MCPD, Farfesa Hassan Ibrahim, ya bayyana cewa shirin horon na shekara-shekara yana zagayawa ne a faɗin Najeriya don ƙara wa mambobin ƙungiyar basira da sanin zamani, musamman a fannin haraji da bin dokokin kudi.

A ranar Litinin, an gudanar da bitar ilimi a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, inda aka bai wa ɗalibai daga sassa daban-daban horo da shawarwari a kan sana’ar akantanci. Shugaban rassa na ANAN a jihar Katsina, Shu’aibu Aliyu, ya bayyana cewa wannan mataki yana nufin karfafa gwiwar matasa su rungumi akantanci tun daga matakin makaranta.

Farfesa Luka Mailafia ya gabatar da kwasa-kwasai da suka yi nazari a kan rawar ANAN wajen ci gaban kimiyyar akantanci a Najeriya, yana mai cewa “ANAN ba kawai hukumar bada takardar shaidar kwarewa ba ce, ƙungiya ce mai cike da hangen nesa da bin ingantattun ƙa’idoji.”

Bayan haka, tawagar ta kai ziyarar girmamawa ga Sarkin Katsina, Dr. Abdulmumini Kabir Usman, CFR, da Sarkin Daura, Dr. Umar Farooq Umar, CON, inda aka tattauna kan shugabanci na gaskiya, bai wa matasa dama da rawar akantoci a amintaccen mulki.

Tawagar ta kuma ziyarci muhimman wuraren tarihi da suka haɗa da Hasumiyar Gobarau da Rijiyar Kusugu da ke Daura, a wani bangare na wayar da kai kan tarihin Hausawa da al’adar cigaba ta hanyar ilimi.

Shugabar ANAN, Hajiya Talatu Kishimi, ta isa Katsina tare da manyan jami’ai da shugabannin rassa daga jihohi daban-daban a ranar Lahadi, 6 ga Yuli, domin kaddamar da zaman horon shekara-shekara na MCPD.

An karɓe su a Filin Jirgin Saman Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, inda aka shiryawa mambobin ANAN damar karɓar sabbin bayanai, halartar kwasa-kwasai da kuma gabatar da bukin rantsar da sabbin mambobi.

Shirin MCPD wani muhimmin mataki ne na gina kwarewa da sabunta ilimi ga dukkan mambobin ƙungiyar, tare da tabbatar da bin ƙa’idojin aiki, dokokin haraji da nagartar gudanar da kudi a matakin gwamnati da kamfanoni.

Taron horarwar MCPD a Katsina ya zo ƙarshe cikin nasara, tare da fatan alheri da tsare gaskiya ga dukkan mahalarta. Mambobi sun bayyana gamsuwa da abubuwan da suka koya, yayin da shugabancin ƙungiyar ya sake jaddada kudurin ci gaba da inganta sana’ar akantanci a Najeriya da ƙasashen waje.

A karkarewa, sakon da aka tafi da shi shine:
"Kwarewa, gaskiya da cigaban kai su ne ginshikan ANAN don gina Najeriya mafi kyau."

Taron ya kammala tare da cikakken wakilcin jaridar Katsina Times don sheda yadda Bikin ya kasance.

Follow Us