Gwamna Lawal Ya Kaddamar Da Rabon Takin Zamani Ga Manoma 59,205 a Zamfara

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09072025_214749_FB_IMG_1752097611037.jpg

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kaddamar da rabon kayan aikin noma na damina na shekarar 2025, ciki har da buhunan taki 59,205 ga manoma a fadin jihar, a wani bangare na shirin gwamnati na bunkasa harkar noma da tabbatar da ingantaccen abinci a jihar.

An gudanar da bikin a ranar Laraba a harabar Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Jihar Zamfara da ke Gusau, inda gwamnan ya kuma bude sabon ginin ofishin Fadama da aka gina domin karfafa hadin gwiwar masu ruwa da tsaki a harkar noma da ci gaban karkara.

Da yake jawabi yayin bikin, Gwamna Lawal ya bayyana noma a matsayin ginshikin tattalin arzikin jihar Zamfara, yana mai cewa fiye da kaso 85 cikin 100 na al’ummar jihar na dogaro da noma don samun abin rayuwa.

“Noma ba kawai sashen tattalin arziki ba ne, shi ne asalin wayonmu da abin da ke bayyana mu a matsayin jama’a. Shi ne jinin tattalin arzikin jihar nan,” in ji Gwamna Lawal.

Ya ce gwamnati ta zabi taken “Noma Alfaharinmu Ne” don jaddada mahimmancin aikin gona ga cigaban jihar, tare da bayyana cewa gwamnati na daukar matakan inganta tsarin noma ta hanyar samar da ingantattun iri, taki, magungunan kashe kwari, da kuma horar da manoma.

Kayayyakin da aka raba sun hada da:

* Buhuna 59,205 na taki daga manyan motoci 98
* Kilo 34,800 na irin shinkafa
* Kilo 80,000 na irin masara
* Lita 23,740 na magungunan kashe ciyawa
* Lita 11,735 na magungunan kashe kwari
* Sakwani 23,470 na sinadaran busar da iri

Gwamna Lawal ya ja kunnen manoma da kada su sayar da kayan da aka ba su, yana mai cewa “wadannan kayayyaki ba su dace da kasuwanci ba. Kayan aiki ne na habaka noman ku da tabbatar da makomar ku da ta jihar Zamfara. A yi amfani da su yadda ya dace, domin su amfani al’umma baki ɗaya.”

Ya kuma bayyana cewa, duk da kalubalen da sauyin yanayi da kuma jinkirin shigowar damina ke haifarwa, gwamnatin jihar na ci gaba da daukar matakai domin tallafa wa manoma da kayan more rayuwa da na zamani.

Gwamnatin Zamfara ta kuma bayyana cewa, tsarin rabon kayan aikin na bana ya shafi manoma 59,205, tare da daukar matakan tabbatar da gaskiya da adalci ta hanyar amfani da tsarin zamani na raba kayayyaki don dakile karkatar da su zuwa hannun 'yan kasuwa.

Gwamna Lawal ya jaddada kudurin gwamnatin sa na tabbatar da cewa harkar noma tana taka muhimmiyar rawa wajen yaki da talauci, samar da ayyukan yi da kuma cimma muradun cigaban dorewa na Majalisar Dinkin Duniya, musamman SDG 2 wanda ke da nufin kawar da yunwa da bunkasa ingantaccen noma mai dorewa.

Follow Us