Jam'iyyar haɗaka ta ADC ta yi Allah wadai da mummunan harin da 'yan bindiga suka kaiwa Masallata a garin gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina
Jagaran haɗakar jam'iyyar ADC a jihar Katsina Dakta Mustapha Inuwa ya nuna baƙin cikin sa game da hari na wuce gona da iri da 'yan bindigar suka kai a daidai lokacin da masallata suke tsaka da yin Sallah
Madugun adawar ya yi kira da kakkausar murya ga gwamnatoci da hukumomin tsaro da su dauki mataki na gaggawa akan wannan matsala da ta addabi al'umma.
Haka kuma Dakta Mustapha Inuwa ya zargi mahukunta da yin sakaci da matsalar tsaro musamman jami'an tsaro da ba sa iya zuwa wuri sai bayan an kai hari sannan su zo.
Dakta Mustapha Inuwa ya ce yin Allah wadai kaɗai bazai isa ba dole sai an ɗauki ƙwaƙwaran mataki kafin abin ya ida ɗaiɗaita Katsina da arewa maso yamma.
Jagoran haɗakar ADC ya nuna buƙatar da ake da ita na kawo ƙarin jami'an tsaro a waɗannan wurare sannan an sanya gaskiya da amana wajen kashe kuɗaɗen al'umma ga jami'an tsaron.
Kazalika ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakan akan wannan matsala ta 'yan bindiga sannan a samar da abubuwan tallafi ga iyalan waɗanda wannan iftila'i ya shafe
Dakta Mustapha ya ja hankalin al'ummar jihar Katsina da su kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya wajen ɗora duk wani alhakin rashin tsaro ga shugabanni
Madugun adawar ya yi addu'ar Allah ya jikan waɗanda suka rigamu gidan gaskiya tare da yin kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da ɗauki matakin ba sani ba sabo akan wannan matsala.
Daga karshe ya yi bayanin cewa lokaci ya zo da za a baiwa harkar tsaro fifiko da yin adalci saɓanin alƙawuran ƙanzon kurege da aka yi al'umma