…Binciken Jaridun Katsina Times
Daga Wakilanmu
Wani bincike da jaridun Katsina Times suka gudanar a wasu ƙananan hukumomin Jihar Katsina ya gano zarge-zargen tafka maguɗi, algus da kuma choge a shirin auren gata da aka yi ikirarin gudanarwa.
Binciken ya yi kira ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Katsina da ta gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka amfana da shirin, tare da yadda aka zaɓo maza da matan da aka haɗa aure.
Haka kuma, binciken ya gano cewa kayan ɗakin da aka tanadar wa amaren ba su kai ƙimar kuɗaɗen da aka ware domin yin su ba. Wannan ya haifar da zargin cewa ko dai kafintocin da suka yi aikin sun yi son rai, ko kuma wasu ’yan kwangila sun yi anfani da kuɗaɗen aikin ta hanyar da ba ta dace ba.
Jaridun Katsina Times sun gano cewa a jihohi kamar Kano da wasu sassa na ƙasar nan inda irin wannan auren gata ya samu nasara, an ɗora jagorancin shirin ne a hannun manyan malamai masu mutunci da kima a cikin al’umma.
Sai dai a Jihar Katsina, gwamnatin jihar ta haɗa hukumomi uku domin gudanar da shirin. Hukumomin sun haɗa da Hukumar Hisbah, Ma’aikatar Addini ta Jihar Katsina da kuma Ma’aikatar Harkokin Mata.
Binciken ya nuna cewa Ma’aikatar Harkokin Mata ta karɓi wasu muhimman ayyuka na shirin, ciki har da kula da kayan ɗaki.
Haka kuma, akwai ƙwaƙƙwaran zargin cewa an haɗa wasu auratayya tare da shelanta daurin aure ne kawai domin a samu damar bai wa wasu kayan ɗaki da sadakin da aka ware.
Binciken ya kuma gano cewa hukumomi hudu ne suka raba fom ɗin neman shiga shirin auren. Hukumomin sun haɗa da Hukumar CDC, Ma’aikatar Addini, Hukumar Hisbah da kuma Ma’aikatar Harkokin Mata ta jihar.
Rahoton binciken ya nuna cewa Hukumar Hisbah ta yi ƙoƙarin tantance waɗanda suka cancanci shiga shirin da kuma waɗanda za a aurar, yayin da Hukumar CDC ta haɗa kai da jami’an ƙananan hukumomi wajen gudanar da wasu ayyukan shirin.
A ƙarshe, binciken Katsina Times ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike domin tsarkake wannan aiki na alheri da gwamnatin jihar ta ƙaddamar.
Munyi kokarin magana da hukumomin da abin ya shafa babu wanda muka samu .mun aika ma wasunsu da sakon kar ta kwana babu amsa ,har zuwa hada rahoton nan.
A watannin baya ne gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da shirin gudanar da auren gata ga marasa galihu masu buƙatar aure. A cikin shirin, an bayyana cewa gwamnati za ta samar da sadaki da kayan ɗaki ga ma’auratan, tare da kashe sama da naira biliyan ɗaya wajen aiwatar da shirin.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page ..katsina city News
Facebook page ..jaridar taskar labarai
07043777779