‘Yan Bindiga Sun Sako Mutum 37 da Aka Yi Garkuwa da Su a Bakori

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29112025_160654_FB_IMG_1764432412670.jpg



An sako mutane 37 da aka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina, bayan ci gaba da tattaunawar zaman lafiya da ake gudanarwa tsakanin jami’an gwamnati da bangarorin Fulani a yankin.

Shugaban Karamar Hukumar Bakori tare da dan majalisar yankin, Hon. Kandarawa, sun jagoranci tarbon mutanen da aka kubutar, bayan jagoran sasancin Fulani, Alhaji Isya Kwashen Garwa, ya mika su ga jami’an gwamnati.

Rahotanni sun ce tawaga daga Bakori, karkashin jagorancin sakataren Karamar Hukumar Faskari, Hon. Bishir Maigora, ta shiga dajin da lamarin ya faru domin karɓar mutanen da aka sace a wurare daban-daban.

Sakin ya biyo bayan ci gaba da tattaunawar sulhu da ake yi da bangarorin Fulani da nufin rage tashin hankali da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a Bakori da Faskari.

Follow Us