Jami’ar Tarayya Ta Dutsin-Ma Ta Dakatar Da Dalibai 20 Kan Satar Jarabawa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12032026_214139_images-57.jpeg

 KatsinaTimes | 12 ga Maris, 2026

Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da ke Jihar Katsina ta dakatar da dalibai 20 daga karatu, bayan samunsu da laifin aikata satar jarabawa ta hanyoyi daban-daban.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Nasiru Abdul, ya fitar ga manema labarai a Katsina ranar Alhamis.

Abdul ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne a yayin taro na 138 na Majalisar gudanarwar jami’ar da aka gudanar ranar Laraba.

Ya ce majalisar ta yanke hukuncin ne bayan nazarin rahoton Kwamitin Ladabtar da Dalibai, wanda ya binciki zargin satar jarabawa da aka yi wa daliban.

A cewarsa, Mataimakin Shugaban jami’ar kuma Shugaban Majalisar, Farfesa Mohammed Khalid-Othman, ya ce an dauki matakin ne bisa dokokin jami’ar da suka shafi gaskiya da bin ka’idojin ilimi.

Ya kara da cewa an yanke hukuncin ne bisa tanadin sashe na 13.3(c) na dokokin jami’ar da suka shafi rashin bin ka’idojin jarabawa da kuma laifukan ilimi.

Sanarwar ta ce Mataimakin Shugaban jami’ar ya yaba wa mambobin kwamitin ladabtarwar dalibai kan kokarinsu da jajircewarsu wajen tabbatar da bin dokokin jami’ar.

Haka kuma ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da binciken cikin adalci, gaskiya da tsauraran matakai.

Abdul ya kara da cewa matakin da majalisar ta dauka na nufin aika sako ga dalibai kan muhimmancin bin dokokin jarabawa da kuma hana wasu aikata irin wannan laifi a gaba.

Ya ce dukkan daliban da abin ya shafa an ba su damar bayyana gaban kwamitin ladabtarwar domin kare kansu kafin a yanke hukunci na karshe.

Follow Us