@ katsina times
Taron da jam iyyar ADC ta jahar katsina ta kira garin Daura ranar jumma a, 13 ga watan March. An tashi baram baram kuma ya bar baya da hayaki.
Taron wanda aka yi shi a wani wurin taron jama a mai suna Arena. an kira shi ne, domin yi ma "yan jam iyya, bayanin muhimmacin rijistar jam iyya da kuma bayar da katin jam iyyar ga duk masu bukata.
Abin da ya kawo rikicin shine salon yadda za a yi rijistar da kuma yadda za a rabar da katin na jam iyyar ta ADC.
Sanata Babban Kaita, daya daga cikin jigon jam iyyar shine aka fito da tsarin za a raba katin jam iyyar da shigar da sunayen mutane a rijistar jam iyyar ta hannun yaransa dake dukkanin kananan hukumomin shiyyar Daura.watau yankin sanata ta Daura.
Wannann tsarin shine ya hassala mutanen Lawal Daura ,manyansu ,matasansu har da kananan su ,suka tashi suka ce sam basu yarda ba.
Wannnan hayaniyar ita tada taron, ba tare da anyi shirin tashi ba.kuma ba tare da an cimma nasarar me aka zo yi a Daura ba.
Mutanen lawal Daura sun hargitsa taron da bakaken maganganu ga dattawan da suka halarci taron.
Muna da bidiyon hayaniyar da akayi kaje shafin katsina city news na Facebook don ka kalla ko katsina times you tube channel.
Katsina times
Www.katsinatimes.com
Facebook page .katsina city News
All social media handles. Katsina times
07043777779.