..... Ta Karbi Kwamitin Bincike Akan Rigimar Da Aka Fuskanta Tsakanin Al'ummomin Rijiyar Tsamiya Da Minawa
Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa wani Kwamiti da zai bada shawarwari akan yadda za'a raba gandun daji da aka karbe daga hannun mutanen da suka mamaye su ba bisa ka'ida ba a fadin Jihar.
Sakataren Gwamnatin Jiha Malam Abdullahi Garba Faskari ne ya kaddamar da kwamitin a madadin Gwamna Dikko Umaru Radda, a Ofishin shi da ke Sakatariyar Jihar Katsina.
Mambobin Kwamitin sun hada da Kwamishinan Filaye Da Tsare-Tsare Dr.Faisal Umar Kaita a matsayin Shugaba sai Kwamishinan Noma Da Kiwon Dabbobi a matsayin Mamba tare davDarktan Gandun Daji wanda shima zai kasance a matsayin Mamba.
Sauran sun hada da Shugaban Kwamitin Maido da Gandun Daji da aka mamaye, Wanda shima zai kasance a matsayin Mamba, a Yayin da Ofishin Gwamnan Jiha zai samar da Sakataren Kwamitin.
Nauyin da aka dorawa Kwamitin ya hada da tantance wadanda suka nuna sha'awar su na neman dazukan da aka kwato, tare da tantance adadin kudin da ya kamata su biya da tsawon lokacin da zasu yi amfani da dazukan.
Haka zalika, an dorawa Kwamitin alhakin tabbatar da duk wanda ya nemi dajin yana da duk takardar da ake bukata, tare da tabbatar da sun sanya kudin da ya kamata su biya a asusun Gwamnati da ya kamata.
Kwamitin zai tabbatar da duk Gandun Dajin da wani mutum ya karba sai da aka samu amincewar Gwamnan Jiha.
Sakataren Gwamnatin Malam Abdullahi Garba Faskari ya bukaci Mambobin Kwamitin akan su yi aiki tukuru wurin sauke nauyin da aka dora masu, domin kawo cigaban Jihar nan.
Shugaban Kwamitin Dr.Faisal Umar Kaita ya yabawa Gwamna Dikko Radda akan wannan dama da aka basu na bada gudummuwa ta wannan fuska, sai ya sha alwashin cewa zasu yi bakin kokarin su wurin sauke nauyin.
A Wani labarin kuma, Kwamitin da Gwamnati ta kafa domin bada shawarwari akan yadda za'a kauracewa fadace-fadace tsakanin al'ummomin Rijiyar Tsamiya da Minawa a Kananan Hukumomin Sandamu da Dutsi ya gabatar da rohoton shi ga Sakataren Gwamnatin.
Shugaban Kwamitin wanda kuma shine Mai ba Gwamna Shawara akan Ayyukan Kananan Hukumomi Alhaji Lawal Rufa'i Safana, tare da Mambobin Kwamitin ne suka gabatar da rohoton nasu ga Sakataren Gwamnatin.
Sakataren Gwamnatin Malam Abdullahi Garba Faskari ya bayyana godiya ga Mambobin Kwamitin akan yadda suka yi aiki ba dare ba rana domin ganin sun bada shawarwarin su ga Gwamnati ta wannan fuska.
Ya Bada tabbacin cewa, Gwamnatin Jiha zata yi aiki da shawarwarin Kwamitin, musamman ma na taimakawa wadanda suka yi asarar dukiyoyi a lokacin fadace-fadacen.
Shugaban Kwamitin Alhaji Lawal Rufa'i Safana, ya bayyana godiyar su ga Gwamna Dikko Radda akan damar da aka basu domin su bada gudummuwar su ta wannan fuska.