CECE-KUCE KAN MAGANAR SAKIN Y’AN TA’ADDA A JIHAR KATSINA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12012026_130136_FB_IMG_1768222580725.jpg


Daga Maiwada Dammallam 

A baya bayan nan babu abinda ya dauki hankalin al’umma kamar labari da ya fito da jaridar Sahara Reporters mai dauke da cewa gwamnatin Jihar Katsina ta shiga yarjejeniyar sakin wasu yan ta’adda kimanin mutum 42 wadanda ke tsare a hannun hukumomi don gurfana gaban kuliya. 

Mutane da dama sun bugo man waya, wasu kuma sun zo takanas sun same ni, suna so su ji ba’asin maganar. Da yawan su sun nuna bacin rai kan wannan mataki da suka ji gwamnati za ta dauka. Nayi masu bayanin kamar yadda zan kara yin bayani anan. 

Da farko dai nayi kokarin su fahimta cewa maganar tsaro magana ce mai bukatar sirri; ba magana bace wadda ta dace da dandalin yanar gizo ko wadda za ayi da gama garin mutane ba. Magana ce wadda ke bukatar sirri da kuma bukatar abu biyu: Na farko fahimce ta sosai kafin a yanke hukunce anyi daidai ko akasin haka, na biyu kuma Ya zamanto an samu mafi sahihancin bayani kan lamarin da ake tattaunawa. 

Ko a gwamnatance, maganar tsaro ba kowa da kowa ke sanin abinda ake ciki ba, ba kuma kowa ake sawa ba. Wannan kuma ba’a Katsina kawai wannan tsarin yake ba. Duk duniya ko ina haka abin yake. Da yawa mutum zai ga maganar tsaro kamar tayi gabas, sai ya bi ta; yayi gudu ya gaji sannan ya gane ashe yamma maganar tayi. 

Gwamanti na da talala kan maganar tsaro. Da yawa mutane sai suga kamar wani munafunci ko son zuciya ke sa gwamnati ba ta fitowa ta fadi mai take ciki kan maganar tsaro. Ba kuma haka bane. Da yawa bayanin ba na fitarwa bane don yana cikin shirin ta na sirri na samun nasarar abinda tasa a gaba. Da yawa abinda mutane suke so su ji daga bakin gwamnati, idan ta fito ta fadi abun to baya da sauran amfani an kan tsarin ta. Akan maganar tsaro gwamnatoci har karya suna iya yi don al’umma su zauna lafiya. Misali, Yau idan gwamnati bata da kudin sayen harsashi don ba jami’an tsaro, tana iya karya tace ta sawo harshashi na biliyoyin naira don taci da buguzum ta tsoratar da abokan fada. To lallai akwai bukatar a fahimta cewa maganar tsaro ta wuce a baje a a jaridu ko a yanar gizo. 

Akan wannan dambarwar, abinda ya faru shine:

Kowa yasan shiri da Kananan Hukumomi daban daban suka shiga na sulhu da yan’ta’adda don samun zaman lafiya. Duk da cewa gwamnati ta dauki matsayar cewa ba zata nemi wani dan ta’adda tayi zaman sulhu da shi ba,  bata rufe Kofar sulhu da duk wani dan ta’adda da yaga kyautatuwar ya aje makami, ya rungumi zaman lafiya ba. Akan haka gwamnati ta saurari bukatun mutane daga Kananan Hukumomi daban-daban da suka zo neman a basu damar su yi zaman sulhu da y’an ta’addan da suka nemi ayi hakan. Gwamnati ta basu damar yin hakan tare da tabbacin bada goyon baya duk inda hakan ya dace kuma ta duk hanyar da bata sab’a ma doka ba. 

Hakan yaba Kananan Hukumomi daban-daban dama suka assasa zaman sulhu da y’an ta’addan da suka addabe su; kuma cikin yardar Allah aka samu nasarorin kawo zaman lafiya a wurare daban-daban ta inda har wurare da ada babu mai iya shiga, yanzu kowa na shiga ya fita cikin aminci da zaman lafiya. Hakkokin yau da kullum sun dawo a wurare da yawa. Kasuwanni da aka rufe a dalilin rashin tsaro, gonaki da aka bar zuwa duk a dalilin rashin tsaro, yanzu duk an koma ana ta hada-hadar yau da kullum. 

A baya, lokacin zaman sulhun, akwai bukatu da Bango tin biyu suka gabatar ma juna don tabbatar da zaman lafiyar da aka samu. Ciki akwai bukatar da al’umma suka ba y’an ta’adda ta sakin duk wani wanda ke rike a hannu su don amsar kudin fansa. Y’an ta’addan kuma sua yarda cewa zasu sako duk wanda ke hannun su tunda yanzu ance sulhu akayi kuma zaman lafiya da yarda da juna za’a ci gaba da yi. Ana su bangaren kuma sun bukaci gwamnati ta sako masu wasu mutunen dake hannun hukumomi suna jiran kuliya. Shugabanni Kasa da na Kananan Hukumomi wadanda suka jagorin ci zaman sulhun suka ba yan ta’addan tabbacin cewa basu da wannan karfin da zasu zartas da wannan hukuncin amma zasu kai koken gaba don ganin anyi hakan don samun zaman lafiya mai dorewa.

Haka kuma akayi. Kananan Hukumomi daban-daban sun zo sun kawo ma gwamnati koken hakan (kamar yadda gwamnati ta bukata don sa ido kan lamarin), sun kuma nuna muhimmancin cika wannan sharadin don samun zaman lafiya mai inganci. Gwamnati ta tuntubi masana tsaro na cikin gida da na waje kan dadewar yin hakan, duk kuma ta samu tabbacin cewa abu ne da dama duk inda ake neman yin sulhun irin wannan matsalar yana iya bijirowo kuma da yawa ana bada damar hakan don samun zaman lafiya. 

Gwamnati ba tayi kasa a guiwa ba, ta koma neman kididdigar mutanen da ke hannun yan’ta’addar ta kuma gano cewa akwai mutane fiye da dubu a hannun yan ta’adda daban-daban wadanda ba’a san halin da suke ciki ba. Daga nan gwamnati ta yarda zata sa baki a sako mutum 42 na yan ta’addan da ke rike gidan kaso amma sai idan sun fara sakin mutanen da aka tantance cewa suna hannun su rike. Haka kuma akayi. Shugabanni Kananan Hukumomi tare da iyayen kasa da jami’an tsaro a lokutta daban-daban sun karbi mutane da y’an ta’adda suka bada karkashin wannan yarjejeniyar. 

Ta wannan tsarin an kubutar da mutane kamar haka:

Karamar Hukumar Safana mutane 36, Kurfi muten 42, Faskari mutane 136, Sabuwa mutane 310, Danmusa mutane 60, Malumfashi mutane 36, Bakori mutane 125, Musawa mutane 28, Matazu mutene 33, Dutsinma mutene 62, Jibia mutane 31. Ba duka ba kenan. Akwai adadin daban samu ba zuwa yanzu. 

Gwamnati, tare da iyayen kasa an zauna an auna ribar cika ma y’an ta’adda alkawarin da iyayen kasa suka daukar masu na lallashin gwamnati ta dubu kyautatuwar sakar masu mutanen da suka roka a saki, an kuma samu gamayyar cewa ribar sakin mutane ta fi rashin ribar yawa. Kan haka aka dauki matakin cika wannan alkawari. 

Bidiyo da na hado da wannan k’asidar na mutanen da irin wannan tsarin ya kubutar da ne a Karamar Hukumar Malumfashi wadanda tsohon d’an ta’adda Mustapha Babaro ya jagoranci kubutar da su, ya kuma kawo ma iyayen kasa, mutene 36 maza, mata da yara wanda akan haka ya roki gwamnati ta sakar mashi mutum 2 kachal. 

Abin kula:

Gwamnati bata dauki wannan matakin don nuna ko-in-kula da halin da y’an ta’adda suka sa jama’a a baya ba. Ta dauki matakin don shi yafi dacewa da yanayin da aka shiga na ta’azzarar matsalar tsaro da kuma neman yadda za’a zaunar da al’umma lafiya, a tsaida zubda jini da asarar rayuka na ba gaira ba dalili. 

Masu fashin baki daban-daban suna kallon lamarin daga mahanga daya ce kawai — cewa an kama mai laifi amma ance an sake shi. Ba su duba mahangar me ke ribar sakin shi din. Misali, a baya-bayan nan akwai yan ta’adda da akayi sulhu da su, da ke mara ma gwamnati baya wajen yaka tare da dakile hare-hare da wasu y’an ta’adda da basu yadda da tsarin sulhu da ke kokarin kai ma al’umma. Ko kwanan nan an fafata tsakanin Mustapha Babaro da dan ta’aada Audu Doro wanda yakai hari a Karamar Hukumar Malumfashi. Audu Doro dan ta’adda ne da tun lokacin tsohuwar gwamnatin Rt. Hon. Aminu Bello Masari, bai yarda ya karbi goron gayya na zaman sulhun ba. 

Kenan, akwai hikima idan gwamnati ta amince ta goya ma y’an taddan da ake da yakinin cewa sun yarda su zauna lafiya da al’umma ta irin wannan hanyar. Akalla dai yakamata mutane sun yarda cewa idan har gwamnati ta tab’a kama d’an ta’adda, to kau tana iya kara kama shi idan ya sab’a ma sharuddan sakin shi da tasa akayi. Kenan, akwai bukatar al’umma su yi ma gwamnati kyakkyawan zato; su fahimci cewa duk matakin da zata dauka ba da ido rufe za ta dauka ba; sai da tabbatar da cewa shine abinda da ta gamsu shi yafi dacewa da al’umma a yanayin da ake ciki. 

Yau idan da gwamnati na da karfin tuwon da zata iya shiga duk inda y’an ta’adda suke ta yake su ne amma aka ga ta koma kan sasanci har an kai ana musayar fursunoni, to sai a zarge ta da yin sanya. To amma kowa yasan ba haka lamarin yake ba. Gwamnatin Jiha bata da soja ko dan sanda. Ko jami’an tsaro na jeka-nayi-ka da tayi bata da hurumin ba su makamai masu inganci irin wanda y’an ta’adda ke amfani da don dokar kasa ta haramta haka. Kenan, akwai bukatar a fahimci irin daurin talalar da kundin tsarin mulki yayi ma gwamnatocin jihohi a kan maganar tsaro don fahimtar irin halin kaka-ni-kayi da suke ciki. Yin haka ne kawai zai bada damar a fahimci kokarin da suke yi a karkashin tsarin da suke jagoranci. 

Ina so ya zama kalubale ga duk wanda yake jin gwamnati ba tayi daidai ba kan wannan lamarin da yayi kokari ya zagaya Kananan Hukumomi da na lissafa a sama, yaji ta bakin mutanen da ka samu kubutarwa don jin ko su ma basu gamsu da matakin da gwamnati ta dauka ba. Ina da yakinin ra’ayin zai ci karo da na masu fashin bakin da suke kallon abin daga nesa  ta cikin yanar gizo — wadanda basu da alaka ta kai-tsaye da matsalar. 

Zan rufe da addu’ar Allah SWT ya ba shugabannin mu karfin guiwa da hikimar kawo mana zaman lafiya mai dorewa.

Bidiyo:
Mutum 36 kenan da y’an ta’adda suka saki a Karamar Hukumar Malumfashi. Zan saka hotunan wasu Kananan Hukumomin a cikin akwatin martani.

Follow Us