Gwamnatin Katsina Ta Rufe Asibitoci Biyu Saboda Saban Ka’idojin

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06082025_151438_FB_IMG_1754493144443.jpg



...Ta Jaddada Kudurinta Na Gyara Harkar Lafiya a Jihar

Daga Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times

Gwamnatin Jihar Katsina ta rufe wasu asibitoci guda biyu masu zaman kansu da ke cikin birnin Katsina, bisa zargin gudanar da ayyukan jinya ba tare da cikawa ka’idojin bude cibiyoyin lafiya ba, da kuma karya dokokin kula da lafiyar jama’a.

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina ce ta dauki wannan mataki karkashin jagorancin Kwamishinan Lafiya, Hon. Musa Adamu Funtua, a wani atisayen bincike da ta fara gudanarwa a ranar Talata, 5 ga watan Agusta, 2025, don tantance ingancin ayyukan asibitoci masu zaman kansu a fadin jihar.

Cibiyoyin lafiya da aka ziyarta sun haɗa da:

1. Zango Orthopedic Nursing Home
2. Heritage Specialty Clinic
3. Lyfcare Medical Diagnostic Services
4. Amaf Orthopedic & Specialist Clinic
5. M&H Clinic & Maternity
6. Bin Maryam Nursing & Maternity Home
7. G-11 Medicine Store & Dental Emergency
8. Dan Kofa Medicine Store
9. Sahel Medicare Centre

Cibiyoyin lafiyar da aka rufe sun hada da, G-11 Medicine Store & Dental Emergency da Dan Kofa Medicine Store, bayan da aka gano suna gudanar da ayyukan jinya ba tare da cika ka’idojin rajista ba, kana suna kwantar da marasa lafiya ba bisa doka ba.

Ma’aikatar ta umarci wadannan cibiyoyi da su koma ga hukumar lafiya ta jihar domin kammala duk wasu sharuddan da suka wajaba kafin a ba su damar ci gaba da aiki.

Kwamishinan lafiya, Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana cewa ziyarar tantancewar za ta ci gaba a sauran sassan jihar, inda gwamnati ke da kudurin tabbatar da cewa dukkan cibiyoyin lafiya suna bin ka’idojin da doka ta shimfida don kare lafiyar al’umma.

Follow Us