ZAKARAN GWAJIN DAFI:HAJJI 2025 KARKASHIN FARFESA SALEH PAKISTAN

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes23112025_083137_IMG-20251123-WA0013.jpg

Shugaban Hukumar Alhazai Ginshikin Ci Gaba da Walwalar Maniyyata a Nijeriya

Daga
Muhsin Tasi’u Ya’u
22 Nuwamba, 2025
Idongari media

Gabatarwa

A kowace shekara, aikin Alhaji yana ɗaukar dubban ‘yan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya don aiwatar da ɗaya daga cikin ginshiƙan Musulunci. Wannan babban aiki yana buƙatar tsari, gaskiya, da ƙwarewa  abubuwan da suka zama alamar shugabancin Shugaban Hukumar Alhazai na ƙasa.
A ƙarƙashin jagorancinsa, hukumar ta samu sauye-sauye masu muhimmanci da suka inganta tsarin tafiya, masauki, abinci, da kula da lafiya ga maniyyata. Wannan ya tabbatar da cewa aikin Alhaji ya zama abin alfahari ga Nijeriya da dukkan Musulmai.

Gyare-gyare da Sauye-Sauye Masu Tasiri

Tun bayan hawansa kujerar shugabanci, ya aiwatar da gyare-gyare na zahiri da na tsarin aiki da suka kawo sauƙi ga maniyyata.Daga cikin wannan tsare-tsaren akwai:
An Kara Tsabtace Tsarin Rijista, Domin Gujewa Cin Hanci da Almundahana
An samar da horar da maniyyata kafin tafiya, don su fahimci dokokin ibada da tsarin zamantakewa,
An inganta huldar hukumar da hukumomin Saudiyya, domin tabbatar da aminci da jin daɗin maniyyata.
Wadannan matakai sun nuna cewa wannan shugaba ba kawai mai kula da ofis ba ne, mai hangen nesa ne wanda ke son ganin aikin Alhaji yana gudana daidai da ƙa’idar Musulunci da mutuncin Najeriya.

Walwalar Maniyyata na Gaba Da Komai

Babban abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne walwalar maniyyata. A lokutan da wasu ke ganin wannan aiki a matsayin tafiyar ofis, shi yana ganinsa a matsayin ibada da amana. An samu sababbin  tsare-tsare da suka tabbatar da cewa maniyyata suna samun:
Masauki mai kyau da tsabta
Kula da lafiya ta zamani
Abinci mai inganci
Sufuri mai aminci.
A lokuta da dama shugaban hukumar alhazai da kansa yake zagayawa  cikin sansanonin maniyyata yana dubawa kai tsaye don ganin duk wani umarni da ka bayar a rubuce ana aiwatar da shi a aikace wanda wannan alama ce ta an yi dacen shugaba mai kula da al’umma da zuciya ɗaya kuma jajirtacce.

Jagoranci Da Addini

A matsayinsa na malami kuma masani a fannin addini, yana jagoranci bisa tsoron Allah. Wannan halin nasa ne ya jawo masa girmamawa daga malamai da shugabannin addini daga sassa daban-daban na ƙasar.
Ayyukansa sun tabbatar da cewa ibada da shugabanci suna iya tafiya tare, idan aka yi su da gaskiya, tsoron Allah, da hangen nesa. 

Tasirin Ayyukansa a Siyasa da Al’umma

Baya ga aikin hajji, wannan shugaba ya zama murya ta gaskiya a cikin al’umma. Yana kira ga zaman lafiya, haɗin kai, da goyon bayan manufofin gwamnati masu amfani ga jama’a. A siyasance ya kare muradun gwamnati da ke nuni da kishin kasa son al’umma da tausaya musu , inganta tattalin arziki da kiwon lafiya da hada kawunan al’umma na kowacce nahiya da kabila a Nijeriya.
Magoya bayansa sun ɗauke shi a matsayin malami mai kishin ƙasa, wanda ke amfani da matsayinsa wajen haɗa kai, ba rarrabuwar kai  ba, don ya tafi da dukkan baggarori na dariku.

Kammalawa

Shugaban hukumar alhazai ya zama abin koyi ga shugabanni da dama  mutum mai hangen nesa, mai gaskiya, mai amana, kuma mai kishin al’umma. “Duk wanda ya yi aiki da gaskiya, Allah zai tabbatar da darajarsa a duniya da lahira.

Follow Us